Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

4 Yuni 2023

01:57:38
1371001

Jerin Shirye-shiryen Da Ake Cigaba Da Gabatarwa Don Tunawa Da Shekaru 34 Da Wafatin Imam Khumain Qs

Takaitaccen Tarihim Rayuwar Imam Khumaini Qs

An haifi Imam Khumaini Qs a shekara ta 1320 bayan hijira (9/21/1902 miladiyya) a birnin Khumain - mai tazarar kilomita 349 kudu maso yammacin Tehran - a gidan da ya shahara da ilimi da kyawawan halaye da tsoron Allah.

Takaitaccen tarihin rayuwar Imam Khumaini (Qs).

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya kawo maku takaitaccen tarihin Rayuwar Imam Khumain Qs wacee ke dauke da darussa da dama na zamantakewa, ilimi, gwagwarmaya tabbatar da adalci acikin al'ummah.

An haifi Imam Khumaini Qs a shekara ta 1320 bayan hijira (9/21/1902 miladiyya) a birnin Khumain - mai tazarar kilomita 349 kudu maso yammacin Tehran - a gidan da ya shahara da ilimi da kyawawan halaye da tsoron Allah.

Imam yayi karatu tsuhen ilimummuka a birnin Khumaini har ya kai shekara sha tara, ya karanci ilimoma da suka hada da harshen larabci, Mandiki, Usulul Fikihu a wajen fitattun malamai na lokacin.


A shekara ta 1339 bayan hijira (1921 miladiyya) ya shiga makarantar hauza a birnin Arak, bayan ya shafe shekara guda ya yi tana karatu anan, Imam ya yi hijira zuwa birnin Qum domin ci gaba da karatunsa a makarantar hauzarta. 


A can Kum baya ga ci gaba da karatunsa a hannun manyan malaman fikihu da mujtahidai na zamaninsa, ya bada muhimmanci wajen karantar ilmin lissafi da physics da falsafa.

 

Kuma yayin da yake ta himma wajen samun ilimin kimiyya, ya mai da hankali kuma akan samu da halartar darussan Akhlak da Sufanci da duka bangarorinsa a nazarce da a aikace da dukkan matakansa a gurin marigayi Ayatullah Mirza Muhammad Ali Shahabadi, inda ya dauki tsawon shekaru shida yana koya. 


A shekara ta 1347 bayan hijira (1929 miladiyya) Imam Khumaini (r.a) ya fara koyarwa wato tun yana dan shekara ashirin da bakwai, ya karantar da bahasosi na falsafar Musulunci, ilimin falsafa da ilimin sufinci a nazariyya da a aikace da kuma Usulul Fikihu, da Akhlak na Musulunci.


Imam ya zabi (Khadija Hanim) diyar marigayi Ayatullah Thaqafi, ta zama matarsa ​​kuma abokiyar zamansa akan tafarkinsa.


Wanda Sakamakon wannan aure ya zamo an samu Zuriyah kamar haka:


- Shahid Ayatullah Sayyid Mustafa Khumaini (1309-1356 Hijira Shamsi).

Sadikatu Mustafawi (matar marigayi Ayatullah Eshraqi).

- Farida Mustafawi (matar Malam Arabi).

- Fahimah Zahraa Mustafawi (matar Dr. Mahmud Buroujerdi).

- Marigayi Hujjatul-Islam Sayyid Ahmad Khumaini (1324-1373 Hijira Shamsi).

Imam Khumaini (Qs) ya fara jihadinsa a cikar kuruciyarsa, ya kuma ci gaba da yin sa a tsawon lokacin karatunsa da hanyoyi daban-daban da suka hada da yaki da fasadi a cikin al'umma da karkatar da lalacewa halaye. 

Gwamnatin Shah sai ta ga cewa mafi kyawun mafita ita ce korar Imam zuwa wajen kasar Iran.

Ta haka nan ne, daruruwan sojoji na musamman da mayaka su kaiwa gidan limamin kawanya, a ranar 3 ga Nuwamba, 1964 Miladiyya. Bayan an kama Imam an dauke shi kai tsaye zuwa filin jirgin sama na Mehrabad da ke birnin Tehran, daga nan kuma bisa abunda suka shirya tun farko, an kai shi gudun hijira da farko zuwa birnin Ankara (Turkiyya), sannan kuma zuwa birnin Bursa na kasar Turkiyya. 


Jami'an tsaron Iran da na Turkiyya da aka dorawa alhakin sanya ido kan Jagora Imam Khomain Qs sun hana shi yin duk wani aiki na siyasa ko zamantakewa.


Zaman Imam a Turkiyya ya kai wata goma sha daya. A tsawon wannan lokaci, gwamnatin Shah ta yi aiki da zaluncin da ba a taba ganin irinsa ba wajen kawar da ragowar gwagwarmaya a Iran.


Tsarewar tilas da aka yiwa Imam a kasar Turkiyya ya kasance wata dama ce ga Imam da ya yi amfani da ita wajen rubuta littafinsa mai muhimmanci (Tahriril Wasilah), inda a karon farko ya tabo a cikin wannan littafi - wanda ke a matsayin littafi abin koyi a aikace na Imam - game da hukunce-hukuncen da ke da alaka da jihadi, da tsaro, da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, da mas’alolin zamani kala-kala.


A ranar 5 ga Oktoban shekarar 1965 miladiyya ne aka mayar da Imam tare da dansa Sayyid Mustafa daga kasar Turkiyya zuwa gudun hijira na biyu a kasar Iraki, inda suka zauna a birnin Najaf. Kuma tun bayan hijirarsa a birnin Najaf, mai girma Imam, baya ga shagaltuwa da koyar da ilimin fikihu ga matakin bincike na waje da kuma gabatar da tushe na ka'idar tsarin mulkin Musulunci da ke dauke da sunan wilayatul Faqih. Imam ya kasance yana mai bin diddigin da bibiyar al'amuran siyasa da ke faruwa a Iran da duniyar musulmi duk da irin wahalhalun da ake fuskanta, kuma yana da sha'awar samun hanyoyin sadarwa da masu juyin juya hali a Iran.


A ranar 24/9/1978 ne jami'an tsaron kasar Iraki suka yiwa gidan Imam Khumaini da ke Najaf kawanya, tare da sharadanta cewa liman ya dakatar da harkokinsa na siyasa tare da shelanta ficewarsa daga wannan gwagwarmaya, a matsayin sharadin zamansa a kasar Iraki. Amma Imam ya yanke shawarar ci gaba da wannan gwagwarmaya, don haka aka yi masa hijira a karo na uku a cikin shekaru goma sha uku wato 4/10/1978 Miladiyya, don haka ya bar Najaf zuwa Kuwait, amma Kuwait ta ki karbar Imam bisa bin matsin lamba na masarautar Iran. hakanan Imam Khumaini ya binciki yanayin kasashen Musulunci, bayan shawarar dansa Sayyid Ahmed ya yanke shawarar yin hijira zuwa birnin Paris, inda ya isa can a ranar 6/10/1978 Miladiyya, washegari kuma ya sauka a gidan wani dan kasar Iran da ke unguwar "Nofal Le Châtre" ba da jimawa ba, wakilai daga fadar Elysee suka zo don sanar da Imam Khumaini ya ce, shugaban kasar Faransa "D'Estaing" ya jaddada wajibcin cewa Imam ya nisanci duk wani aiki na siyasa inda kuma Imam ya mayar da martani da kakkausan lafazi da cewa irin wannan takunkumin ya sabawa da'awar dimokuradiyya, kuma ko da an tilasta masa tashi daga wannan filin jirgin zuwa wancan, kuma daga wannan kasa zuwa waccan, ba zai bar aikinsa na yada manufarsa ba. 


Don haka zaman da Imam Khumaini ya yi na tsawon watanni hudu a wannan yanki na birnin Paris ya mayar da shi wurin daukar hankalin duniya, kuma cibiyar labarai mafi muhimmanci a duniya. 


Kuma ya kasance yawan lakcocin da Imama ya gabatar da tarurruka da yawa da tawagogi da suka zo daga ko'ina cikin duniya sun taka muhimmiyar rawa wajen fahimtar duniya dangane da ra'ayinsa kan gwamnatin Musulunci da manufofin juyin juya halinsa.


Kuma al'ummar Iran su ma sun kara habaka yunkuri da juyin juya halinsu tare da zuwan sakon nusantarwa daga Imam, inda zanga-zangar da suke yi ta yadu, inda suka afkawa tare da gurgunta cibiyoyin gwamnati, sannan sarki ya maye gurbin firaministansa daya bayan daya, sannan ya sanar da tubarsa kan keta haddin da ya aikata. Sannan ya gabatar da wasu tsofaffin mukarrabansa a gaban shari'a, ya kuma kori wasu fursunonin siyasa, amma duk wadannan ayyuka ba su hana juyin juya hali ya fadada da kuma kara karfi ba.



Imam ya nada Majalisar Shura ta juyin juya halin Musulunci, Inda Sarki ya gudu a ranar 16 ga Janairu, 1979 bisa dalilin rashin lafiya da bukatarsa ​​ta huta, gudun hijirar da ya yi ya haifar da jin dadi da Farinciki a tsakanin al'umma, tare da karfafa azamar gwagwarmaya har zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatin tsarin mulki. 


Matakin da Imam Khumaini ya dauka na komawa Iran ya haifar da farin ciki da jin dadi da fata a cikin zukatan al'umma, lamarin da ya sa makiya juyin juya hali suka yi gaggawar mayar da martani, sannan kuma gwamnatin ta tuntubi Amurka tare da yanke shawarar rufe filayen saukar jiragen sama musamman masu tafiya na kasashen waje. Don haka jama'a daga ko'ina cikin kasar suka nufi birnin Tehran domin halartar miliyoyin mutane a zanga-zangar kiran bude filayen jiragen sama, kuma gwamnatin kasar ta amince da hakan kuma ta bude filin jirgin saman Tehran, don haka jirgin da ya dauko limamin ya sauka a ranar 1/2/1979 Miladiyya bayan shekaru goma sha hudu ya yi gudun hijira.



Cika alkawuran Imam Khumaini (r.a) da nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ba wai wani lamari ne na cikin gida kawai da ya kai ga sauya tsarin siyasa ba, a'a juyin juya halin Musulunci ya kasance kamar girgizar kasa mai muni ga kasashen yammacin duniya.

Ba'a wuce sama da watanni biyu ba da samun nasarar juyin juyi hali har sai da Al'ummar Iran aka sanar da su a daya daga cikin zaben da akai mafi 'yanci a tarihin Iran, nuna goyon bayan da ya bayar da kashi 98.2 bisa 100 na kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.


A tsawon shekaru goma da watanni hudu na rayuwarsa bayan kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam ya kasance mafi kyawu a cikin jagorancin wannan gwamnati da al'ummar Iran wajen fuskantar manyan kalubale, musamman yakin shekaru takwas da Gwamnatin Baath ta kasar Iraki ta dorawa Iran na tsawon shekaru takwas.


Da misalin karfe 22:20 na ranar asabar 3 ga watan yuni shekara ta 1989 miladiyya aka karbi ruhin Imam Khumaini domin ta isa zuwa ga Malakutul A'laa yana dan shekara 87 a duniya. 


An yi jana'iza da bizne Imam a kusa da Aljannar Zahra (Behesht Zahra) kusa da hubbaren shahidan juyin juya halin Musulunci, inda daga baya ake kiran wajen da sunan Haramin Imam Khumaini (amincinsa ya tabbata a gare shi).


Imam ya bar tarihi mai kima na rubuce-rubuce da suka hada da wasiyyarsa ta siyasa da gungun littafi da suka kunshi sassa 22 da sunan "Sahifatul Imam Khumaini." Haka nan kuma an tattara wakokin Imam a cikin litafi mai suna ''Diwan Imam'' kamar yadda aka tattara darussan Imam da ya bayar a makarantar hauza mai taken "Taqrirat Imam Khumaini" Da sauran littafai masu kima a fagen falsafa, siyasa, Akhlak da Usul da sufanci da zamantakewa.