Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

3 Yuni 2023

09:49:59
1370854

Iran: Ta Nuna Alhininta Ga Wadanda Hatsarin Jirgin Kasa Ya Rutsa Da Su A Indiya

Da yake nuna alhinin Iran ga iyalan wadanda hatsarin jirgin kasa ya rutsa da su a jihar Odisha ta Indiya

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran bayan hatsarin da jirgin kasa wanda ya sauka daga layin dogo a jihar Odisha ta kasar Indiya, ya fitar da sako game da wannan mummunan hatsarin ga gwamnati da al'ummar wannan kasa, musamman ma iyalan wadanda abin ya rutsa da su yana mai jajantawa da nuna tausayinsa gare su.