Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

1 Yuni 2023

08:22:35
1370289

An Nuna Fina-finan Iran 2 A Wajen Bikin Fina-finai Na Archaeology A Serbia

Fina-finan dai daya ya shafi rayuwar Kurdawa da dayan kuma na rayuwar Turkmen na Iran, fina-finai ne guda biyu da kasar ta yi, wadanda aka nuna a lokacin bikin fina-finan archaeological na kasa da kasa na kasar Serbia karo na 23 a gidan tarihin kasar nan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, an gudanar da Bikin fina-finan archaeological na kasa da kasa karo na 23 na Serbia tare da halartar fina-finai 22 daga kasashe 6: Girka (2), Italiya (4), Spain (3), Rasha (2), Iran (2) da Serbia (9) bukin wanda aka gudanar da shi a gidan kayan tarihi na Serbia tare da halartar Daniela Vanosic, Mataimakin Ministan Al'adu na Serbia don kare al'adun gargajiya, Breskovic, shugaban gidan tarihi na Serbia, Amirpour, mai ba da shawara kan al'adun kasar Iran, jami'an diflomasiyya na wasu ƙasashe da kuma gungun jama'a masu shaawa sun samu halarta.