Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

31 Mayu 2023

06:32:35
1369928

Amir Abdullahian: Alakar Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa na bunkasa a bangaren gwamnati da masu zaman kansu

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a matsayin amintacciyar abokiyar kasuwanci tare da bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta bunkasa ne a matakin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Husain Amir Abdullahian, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a ganawarsa da Khalifa Shaheen Al Marr, minista mai ba da shawara kan gwamnatin hadaddiyar daular Larabawa, ya yi ishara da manufofin gwamnatin kasar ta 13 wajen raya hulda da juna na makwabtaka, kuma ya ambaci UAE a matsayin amintacciyar abokiyar kasuwanci kuma ya kara da cewa: Kasar tana ci gaba a matakai biyu, gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.