Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Mayu 2023

11:16:30
1369826

An Yanke Wa 'Yan ISIS 23 Hukuncin Kisa A Libya + Bidiyo

Wata kotu a kasar Libya ta yanke wa wasu 'yan ta'addar ISIS 23 hukuncin kisa bisa zargin fille kawunan Kiristoci.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya bayar da rahoton cewa, wata kotu a kasar Libya ta yanke wa mutane 23 hukuncin kisa, yayin da wasu 14 a gidan yari, bisa samunsu da hannu a cikin kazamin farmakin kungiyar ISIS, wanda ya hada da fille kan wasu gungun mabiya addinin kirista na kasar Masar da kuma kame wasu mutane birnin Sirte a 2015 An yanke masu hukunci, wasu guda 14 kuma an yanke masu dauri rai da rai har abada.

Babban mai shigar da kara ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Litinin cewa, an yanke wa daya daga cikin wadanda ake kara hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari, shida wadanda ake kara kuma an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10, daya kuma an yanke masa hukuncin shekaru biyar, sauran shidan kuma an yanke musu hukuncin shekaru uku a gidan kurkuku. Kuma a cewar wannan sanarwa, an sallami mutane biyar daga cikinsu.

Kamar yadda yake cewa Libya na daya daga cikin sansanonin ISIS da ke wajen Iraki da Syria, kuma kungiyar ta yi amfani da hargitsi da yakin da ake fama da shi a kasar da ke arewacin Afirka, wanda kungiyar tsaro ta NATO ke marawa baya bayan boren 2011.

A shekara ta 2015 ne kungiyar ISIS ta kai hari a wani katafaren otel na Corinthia da ke birnin Tripoli, inda ta kashe mutane tara tare da yin garkuwa da wasu Kiristocin Masar da dama.

Bayan samun galaba a Benghazi, Darna da Ajdabiyah a gabashin Libya, kungiyar ta'addanci ta Da'esh ta kwace birnin Sirte da ke gabar teku tare da rike shi har zuwa karshen shekarar 2016.

Daya daga cikin lauyoyin iyalan wadanda abin ya shafa ya ce mu a matsayinmu na lauyoyin iyalan wadanda lamarin ya shafa muna ganin hukuncin da kotun ta yanke ya gamsar da gaske kuma yana da adalci.

Ya kara da cewa: Kotu ta yi Allah wadai da wadanda aka tabbatar da laifinsu, ta kuma wanke wadanda babu isassun hujjoji a kansu.

Fatimah, mahaifiyar daya daga cikin wadanda abin ya shafa, ta shaida wa Al Jazeera cewa ba za ta iya bayyana farin cikinta ba bayan yanke hukuncin.

Inda ta ce: Ya kai dana Muhammad, na sami adalci akan kisanka. Ban iya barci ba tun lokacin da aka kashe 'ya'yana maza biyu. Mun shaida yadda ake gudanar da adalci.