Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Mayu 2023

10:47:49
1369821

Rikici Mai Tsanani Tsakanin Sojojin Yahudawan Sahyoniya Da 'Yan Gwagwarmayar Palasdinawa

Bayan harin da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai a sansanin Tulkarm dake arewacin gabar yammacin kogin Jordan, wani kazamin rikici ya barke tsakanin su da dakarun gwagwarmayar Palasdinawa tare da raunata wani sojan sahyoniyawan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari sansanin "Nur Shams" dake Tulkarm.

Dakarun shahidan Al-Aqsa sun sanar da cewa dakarun gwagwarmayar Palastinawa sun harbe sojojin makiya yahudawan sahyoniya da suka kai hari a sansanin Noor Shams.

An samu fashewar wani abu da kazamin rikici a yayin kazamin harin da sojojin yahudawan sahyoniyawan suka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Noor Shams, kuma wani sojan sahyoniyawan ya jikkata a yayin wadannan gumurzun.