Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

30 Mayu 2023

02:09:25
1369727

Muna Maraba Da Hulda Da Masar

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci: Haɗin Gwiwa Tsakanin Oman da Iran Yana Da Muhimmanci

Haka nan kuma yayin da yake ishara da bayanin Sarkin Oman dangane da aniyar kasar Masar ta sake dawo da hulda da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Muna maraba da wannan matsaya, kuma ba mu da wata matsala dangane da hakan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a yayin ganawarsa da Haitham bin Tariq Al Saeed, Sultan na Oman da tawagarsa a safiyar jiya litinin, ya kira alakar da ke tsakanin Iran da Oman mai dadewa, mai tushe kuma mai kyau, sannan ya ce: Mun yi imani cewa fadada huldar da ke tsakanin kasashen biyu a kowane fanni wanda hakan yana da amfani ga bangarorin biyu.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da shawarwarin da aka yi tsakanin bangarorin Iran da Omani, ya yi nuni da cewa: muhimmin abu shi ne a rika bin wadannan tattaunawar da gaske har sai an cimma sakamako mai ma'ana, daga karshe kuma a fadada huldar.


Har ila yau Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana irin hadarin da ke tattare da kasancewar gwamnatin sahyoniyawan a yankin inda ya kara da cewa: Manufar gwamnatin sahyoniyawan da magoya bayanta ita ce haifar da sabani da rashin zaman lafiya a yankin, don haka dukkanin kasashen yankin yakamata a kula da wannan batu.


Ayatullah Khamenei ya yi nuni da cewa, yana da muhimmanci a kara yin hadin gwiwa a tsakanin Oman da Iran, saboda kasashen biyu suna da tarayya a muhimmiyar mashigar ruwa ta Hormuz.


Haka nan kuma yayin da yake ishara da bayanin Sarkin Oman dangane da aniyar kasar Masar ta sake dawo da hulda da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Muna maraba da wannan matsaya, kuma ba mu da wata matsala dangane da hakan.


Ayatullah Khamenei ya ce dangane da gamsuwar da Sarkin Oman ya yi da maido da huldar dangantaka tsakanin Iran da Saudiyya: wadannan batutuwan sun samo asali ne daga kyakkyawar manufar gwamnatin Dr Raisi na fadada da karfafa alaka da makwabta da kasashen yankin.


A karshe ya bayyana fatansa cewa, idan aka fadada alaka tsakanin gwamnatoci, al'ummar musulmi za su dawo da martabarsu, sannan kuma karfi da kayayyakin da kasashen musulmi suke da shi za su amfanar da dukkanin al'ummomi da kasashe da kuma kasashen musulmi.


A wannan taro, wanda ya samu halartar shugaban kasar Hujjatul-Islam al-Islam Wal-Muslimin Raisi, Sarkin Oman Haitham bin Tariq Al Saeed, ya bayyana matukar jin dadinsa da ganawa da jagoran juyin juya halin Musulunci, wanda ya kira manufar Oman ta fadada alakar da ke tsakaninta da kasashen da ke makwabtaka da ita, musamman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Muhimmin abu. Inda ya kuma ce: A yayin tattaunawar da aka yi a nan Tehran an tattauna batutuwan hadin gwiwa daban-daban da kuma yin musayar ra'ayi, kuma muna fatan ci gaba da wannan shawarwarin, dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu za ta kasance mai kara fadada wanda kuma sakamakon aikin sa zai bayyana ga bangarorin biyu.


.........................