26 Mayu 2023 - 13:29
Al-Mashat: 'Yantar Da Kudancin Lebanon Ya Kasance Wani Muhimmin Mataki Ne

A cikin wani sako da ya aike wa al'ummar kasar, da sojoji da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ta taya murnar " Ranar Gwagwarmaya Da 'Yanci" kudancin kasar Labanon tare da kara cewa: Wannan 'yantowar wani muhimmin mataki ne na dabaru da zaburar da al'umma masu 'yanci a duniya".

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Mahdi Al-Mashat ya kara da cewa a cikin sakon taya murna ga kasar Labanon: Yaman na matukar mutunta wadanda suka kirkiro ranar gwagwarmaya da 'yanci a kudancin Labanon, da kuma shugabanni da al'ummar kasar da suka yi tsayin daka ta wannan hanyar.


Shugaban majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ya bayyana cewa: Ranar gwagwarmaya da 'yantar da kudancin Labanon a matsayin wata dabarar jujjuyawar matakai a dukkan matakai wani abin zaburarwa ne ga masu fafutukar 'yanci na duniya.