26 Mayu 2023 - 13:01
Wani Matashin Bafalasdine Yayi Shahada A Hannun Masu Tsatsauran Ra'ayi A Khalil

Wani matashin Bafalasdine ya mutu a safiyar yau Juma'a sakamakon munanan raunukan da ya samu bayan harbin harsashi daga da ga mazauna a birnin Khalil.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Wannan matashi yana shirin kai hari ga wajen gidan ibadar Yahudawan sahyoniyawan dake matsugunin Tana Omarim da ke kudancin Khalil, sai wani dan Isra'ila ya harbe shi, sakamakon wannan aika-aikar da ya aikata ya samu munanan raunuka a karshe ya mutu.

Wannan matakin yana faruwa ne yayin da sojojin Isra'ila suka aiwatar da tsauraran matakan tsaro a wannan gari saboda fargabar mayakan Falasdinawa na kutsawa cikinsu.