Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

23 Mayu 2023

07:29:09
1367925

Falasdinu: An Jikkata Yahudawa Biyu A Gabar Yammacin Kogin Jordan

Mutane 2 sun jikkata sakamakon harbin da aka yi wa motar ‘yan sahayoniya a gabar yammacin kogin Jordan

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Majiyoyin yankin na Palasdinawa sun sanar a daren jiya Litinin cewa, an harbi wata motar Sahayoniyyawan mamaya a yammacin gabar kogin Jordan tare da jikkata wasu ‘yan sahayoniya 2.

Majiyar masu amfani da harshen yahudanci ta sanar da cewa, wannan lamari ya afku ne a kusa da garin Beita da ke kudancin Nablus, kuma bataliyoyin Fajr daya daga cikin kungiyoyin gwagwarmaya sun dauki alhakin kai wannan hari kan yahudawan sahyuniya.

Bataliya Fajr ta sanar da cewa: Domin daukar fansa kan shahidan, wata tawagar mayakan kungiyar ta kai hari kan wata motar sahyoniyawan kusa da tashar Avitar da ke kudancin Nablus a ranar Litinin din da ta gabata, inda a sakamakon haka aka jikkata wasu yahudawan sahyoniya kuma mayakan mu sun samu nasarar barin wurin ba tare da wata matsala ba.