Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa,
"Nasir Kanaani" ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: "Da wuya ministan harkokin wajen Jamus bai san tunanin al'ummar Iran game da iskar gas da sinadarai da alakarta da gwamnatin Jamus ba."
Kanaani ya yi ishara da cewa gwamnatin Saddam na da makamai masu guba, ya kuma jaddada cewa: Ta yaya shi wanda gwamnatinsa ke da alhakin baiwa gwamnatin Saddam makamai masu guba da kuma kashe dubban 'yan kasar Iran guba, ya bai wa kansa damar yin magana kan lamarin hakkin bil'adama na al'ummar Iran!