Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa,
Ayatullah Sayyid Yassin Al-Musawi limamin Juma'a a birnin Bagadaza ya yi ishara da cewa: Menene ma'anar maganar Amurka na cewa dokar ta baci ta ci gaba da kasancewa a Iraki? Dokar ta-baci na nufin rashin zaman lafiya a Iraki.
Ya kara da cewa: Matakin da Amurka ta dauka na nufin ci gaba da rashin zaman lafiya ga kasar Iraki, wannan ba ra'ayi ba ne! Suna cewa a cikin harshensu, ma'anar ci gaba yana nufin: an riga an sami yanayin rashin zaman lafiya, wato, mu 'yan Iraki ba za mu iya tafiya da kafafunmu ba kenan!