Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

21 Mayu 2023

19:38:06
1367625

Dalibai 197 Ne Maza Da Mata Da Aka Gabatar Da Bikin Yayesu

An Gudanar Da Taron Yaye Daliban Harkar Musulunci Da Suka Hardace Alkur'ani Karo Na 12 A Birnin Kano Najeriya

Dubban Al'umma ne daga sassan wannan kasa dama wajanta suka sami halartar wannan gagarumin taro na mahaddata.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Dama dai duk shekara an saba ana gabatar da wannan taro wanda wannan shine karo na shabiyu.

Ashekarun baya Maulana Sheikh Ibrahim Zakzaky (h) shi ne yake zama Babban bako mai jawabi wanda a wannan karon ma Sheik din ne yazama maijawabi, yayin da aka saka Jawabinsa da yagabatar ga Ba'adin Hafizan yayin da suka kaimasa ziya agidansa dake Abuja.

Kafin jawabin na Babban Bako, tun farko bayan bude taro da addu'a, karatun al'kur'ani, mawaka sun gabatar da wakoki, ciki akwai Shaharrarn Mawakin nan na Sayyida Zahara(as) wato Bashir Dandago, wanda ya gabatar da sabuwar wakar da yayiwa Maulana Sheik Ibraheem Zakzaky(h) sai kuma Abban Malam Mai Sharifiya dukkansu biyun daga Gidan Kadiriyya Asahabulkahafi.


A wajan dai anyi gwajin hardar Dalibai Mahaddatan, inda Gwanayan Alarammomi na ciki da wajan Harka suka gwadasu.

Sai kuma Darasu da aka yiwa Daliban.

Hakama Yara Matasan Abulfadul sun gabatar da waken jaddada bai'a ga Jagoran Zamaninmu Maulana Imamul Mahadi(aj)


Karshe anraba Kyaututtuka ga wasu fitattun Malamai da suka hidimtawa Al'kurani kamarsu Sheik Dahiru Usman Bauci, da Sheik Yahuza Gwani Danzarga, Shiekh Jafar Mahmud Adam, Sheik Kalifa Ishaq Rabi'u, sai kuma kyutar Al'kur'an ga Sheikh Nasiru Kabara, wanda Jikokinsa Sheikh Musubuhu, da Babban Dan Sheikh Abduljabbar suka karba amadadin Kakansu.


An bada kyauta ta musamman ga Mai martaba Sarkin Kano Margayi Dakta Ado Bayaru.


Sai kuma aka bawa Dalibai Shedar kammala karatun alkur'an, inda bangaran Maza Sheikh Abdulhamid Ballo, da Sheik Abdullahi Zango da Farfesa Abdullahi Danladi suka mika musu.

Sai kuma bangaran Mata inda Malama Maimunatu Sheik Turi, da Malama Jamila Sheik.Muktar Sahabi, sai Malama Lubabatu Sheik Sunusi suka basu Shedar hardar ga daliban.

M Imamu kurna yayi jawabin godiya, sai Sayyid Badamsi yayi addu'ar rufewa.

Taron ya sami kyakkyawan tsare inda ma'aikatan dake kula da tsaro wanda suka hada Harisawa da Abul'fadal, da sauran masu taimaka musu suka hadu sukayi aiki karkashin kwamitin tsara taron don ganin an sami nasara. 

Anyi taron cikin nasara Mahalarta sun kama hanyar komawa gidajansu na kusa da nesa.

Abinda ke biye hotuna ne da muka dauko muku.

Muhammad Hadi Jamkad