Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, A wajen wannan biki, Hujjatul-Islam Walm "Muhammad Jawad Muhammadi Golpaigani" ya gabatar da jawabi kuma "Muhammad Reza Gholamrezadeh" ya gabatar da yabo.
Taron da aka gudanar da shi a jiya asabar 20 ga watan Mayu bayan sallar Magriba da Isha'i a gudanar da bikin Maulidin Karimatu Ahlul Baiti Sayyida Fatima Ma'asumah (a.s) a harabar Imam Khumaini (a.s). Dake haramin Shah Abdul Azeem Hasani As Tehran.