Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

14 Mayu 2023

03:30:48
1365454

BA ZA A DAINA CEWA “WAYYO BA” HAR SAI AN GANO ASALIN MATSALA DA HAKIKANIN MAFITA

JAWABIN JAGORA SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR GORON SALLAH SHAWWAL 1444H (29/4/2023)

Da yammacin ranar Asabar 9 ga watan Shawwal 1444H (29/4/2023) ne Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da wasu daga wakilan ‘yan uwa a gidansa da ke Abuja. Abin da ke tafe rubutaccen jawabin da ya gabatar ne, wanda CIBIYAR WALLAFA Da Yada Ayyukan Jagoran ta rubuto muku.

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, ya kawo maku jerin jawabai da jagoran harkar musulunci a Najeriya ya gabatar a lokacin Ziyarar sallah Karama data gabata kamar yarda cibiyar yada karatuttukan da bayanan Shekh din suka kawo manufarmu anan shine kai wannan sako ya isa ga ga Al'ummar duniya gaba daya ya zmao sun anfana daga bayanan jagora Hafizahullah.


GABATARWA:

A’uzu billahis Sami’il Alim, Minas shaidanir rajim, Bismillahir Rahamanir Raheem. Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyina wa Habibi Qulubina Abil Qasimi Mustapha Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahirinal Ma’asumiyn, Siyma Baqiyatullahi fiyl ard, Sahibul Asr waz Zaman arwahuna lahu fidah.


Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa barakatuh.


Asalin wannan zaman namu saboda barka da sallah ne (Idil Fidr) na shekarar 1444. To, idan yadda ya kamata ne, ya dace ace kamar bayan sallah da kwana daya ne ko da kwana biyu (aka yi zaman), amma saboda sha’anin yadda abubuwa suke tafiye-tafiye da sauransu, sai ya zama da dan jidali a ce nan da nan daga yin sallah a zo. 


Dama dai irin yadda muke yi da ne, kun san ranar Sallah ma mu kan zauna, haka kashegari ma, duk dai ranakun bayan sallah mu kan dan zazzauna. Sannan kuma mu kan dan yi wasu bayanai haka bayan sallah da kuma lokacin ma sallar.


To na san dai zuruf ba su iya bamu damar yin hakan ba. Saboda haka dai, na san na yi sakon Quds, amma sakon sallah sai dai idan yanzu ne za a ji. Saboda haka sai na fara da taya mu murna kenan da kammala Azumin watan Ramadan na wannan shekara da kuma ganin wannan Idi na karamar Sallah.


AL’UMMA BATA FAHIMCI MENE NE MAFITARTA BA


Na’am, na san ko bara mun ce muna cikin mawuyacin hali. Wani irin yanayi muka samu kanmu a ciki, kuma dai yanayin ba sakewa ya yi ba, yana nan yadda yake, idan ma ba dada tabarbarewa ya yi ba. Ko ba haka nan bane? Kun san abubuwa gyaruwa suke yi ko dada lalacewa? Abubuwa sai dada lalacewa suke ta yi. To kuma abin bai sake ba, sai dai muni ma yake ta ta yi, yanayin kenan.


Kuma al’umma tana cikin baganniya, bata gane wai mene ne ya sa ta fada cikin halin da ta fada ba, kuma meye mafita? Na kuma san tun shekarun baya mun sha batun cewa idan kana batun matsala, kowa ka yi magana da shi za ka ga ya san matsala, amma meye musabbabin matsala, mene ne kuma magani? To nan ne za ka ji maganganu mabambanta, wannan yace kaza, wannan yace kaza.


BA ZA A DAINA CEWA “WAYYO BA” HAR SAI AN GANO ASALIN MATSALA DA HAKIKANIN MAFITA


To, mun godewa Allah, akalla kaga dai cikin ni’imar da Allah Ta’ala ya yi mana, ya nuna mana hanya. Mun gode masa. Ba za mu iya cewa bisa hadari bane, bisa tagomashi ne daga wajensa. 


Na’am, mun wayi gari ne muka gammu (a matsayin) ‘ya’yan iyayenmu Musulmi. To amma idan mutum ya lura, kusan dan abin da ya rage shine dan abin da ya rage na abin da bamu gama lalatawa ba, na wadanda kakanninmu suka yi mai kyau. Su suka yi aikin kirki ya wanzu, kuma tun lokacin sai muka yi ta lalatawa, muka yi ta lalatawa, to bamu gama lalatawan bane, shine a ka samu dan abin da aka samu a yanzu. 


To kuma kamar su mutane suna tunanin shikenan haka za a yi ta tafiya. Idan kace musu to wai ba mafita ne? Ko su ce maka babu mafita, ko kuma su kawo maka mafitan da ba ita ce (hakikar) mafita ba.


Na san bara ina cewa, kullum idan ka tambayi mutane mafita? Sai su ce maka to a jira sai an yi zabe. Sai an zabi shugaba mai adalci, sai ya gyara, sai a huta. Har nace to ba irin wannan ne kuka yi ba shekarun baya? Sai da kuka darje waliyi zanqalele? Kuma yanzu ya kwashe shekara takwas yana ta muku gyara, sannan kuma sai kuna wayyo-wayyo? 


To har bara nake cewa to wa ya sani, idan aka sake irin wannan? A bara nake cewa, su suna cewa sai a jira 2023. Yanzu gashi 2023 din ta iso, har ma an yi zaben ko? Nake cewa to yanzu wa ya sanar da ku ko ma sai kun sake cewa wayyo? Wa ya sanar da ku ko ma sai kun ce ina ma tsohon waliyin nan ya dawo? Saboda yadda abubuwa suka zama.


Ba haka nake fata ba, amma tana iya yiyiwu ya zama hakan ai. Wa ya tsammaci abin da ya faru yanzu zai faru? Ai da mutane sun dauka mafita suka samu ko? To sai suka ga abin da suka samu. To wa ya sanar da su ko nan gaba abin da za su gani sai sun sake cewa wayyo? To, wayyo kam gaskiyar magana, yana da wahalar gaske a bar wayyo din nan har sai ranar da aka gane cewa wai mene ne asalin lalacewar nan kuma mene ne mafita?


Jawabin Jagora Shaikh Zakzaky (H) Yayin Ziyarar Goron Sallah (5)


DANGANE DA RIKICIN SUDAN


Sudan yanzu kun ga yadda ake ta faman rikici ko? To a da ai ana rikicin tsakanin Kudu ne da Arewa ko? Ana nan aka ce Kudu su zama kasar kansu, suka zama kasar kansu. To su masu haddasa rigimar da suka ga Kudu yanzu ba za su iya kawo musu rigimar addini ba saboda mafi yawansu ba Musulmi bane, mafi yawansu addinin gargajiya suke yi, in ma za a raba su ta fuskacin addini to idan kace masu addinan gargajiya, da yake addinin gargajiyan ba addini daya bane, addinai ne daban-daban. To idan kace masu gargajiya sune na daya, daga su sai Musulmi, kirista sune ‘yan kadan, duk da su kiristan su kan rika magana da yawun duk wanda yake ba Musulmi ne ba. 

 

 To da sun yi ta ingiza su a kan cewa su ‘yan Kudu kiristoci ne su, kuma Musulmi sun danne su, to yanzu su yanzu su ‘yan Kudun su yasu ne, ba zai yiwu su haddasa musu rigimar addini ba, sai suka koma suka haddasa musu ta kabila. Domin akwai su da arzikin mai, da arzikin noma, amma suna fama da talauci. Ka ga mutum bashi da ‘kubz’ da zai ci, amma yana da A.K da jigidan harsashi. Farashin wannan bindiga da harsashin zai ciyar da shi abincin shekara amma bashi da na yini, duk ga kashin awazansa a waje amma yana da bindiga a cikin rumfar ciyawa a dokar daji, ana fadan kabila tsakanin Dinka da Nuer. To amma inda ake dibar man lafiya lau.


 To yanzu suma Arewan an samu wata rigima an maka musu ko? Ana ta harbin al’umma ba ji ba gani. Kuma wani abin mamaki, wai masu harbin sai suna cewa “Allahu Akbar!” Mutum yana harbi yana kashe Musulmi wai yana cewa “Allahu Akbar. To wane ne yake tare da Allahu Akbar a cikinsu? Wa ke wakiltan Allahu Akbar? Ana dambara harsashi ne a kan mutanen da basu ji ba basu gani ba. 


 Kuma idan ka bibiya, na waje suna da hannu a kowanne, kowanne akwai wanda ke mara musu baya. Ba bindiga ko guda daya da aka (kera) a Sudan, ba harsashi ko daya da aka yi a Sudan, amma su wa ake kashewa a Sudan? Su waye? Musulmi ne a Arewacin kasar. Don amfanin wa? Don amfanin Sudanawa? Don amfanin makiyansu ne. To irin rigingimun kenan, a bullo da wannan a bullo da wannan.


RIKICIN TUTSI DA HUTU A AFIRKA TA KUDU


Wani abin da ko a mafarki mu a nan ba za mu taba yinsa ba, na san lokacin da wasu Fulani suka zo nan na yi wannan maganar, nace ina jin karshen 1999 ne na tafi Afirka ta Kudu don wani taro a Pretoria, lokacin ana tsaka da rigima ne tsakanin Tutsi da Hutu (ban san ko ya suke ambatonsu da harshensu ba), kabilu ne guda biyu; Tutsi da Hutu. Hutu wasu mutane ne haka, kabila ce galibansu ‘yan gajajjeru ne masu dan jiki, sannan kuma su Tutsi wasu siraran mutane ne dogaye masu siririn hanci haka. Su Hutu manoma ne, su kuma Tutsi makiyayan dabbobi –musamman shanu- ne. 


To sai aka hada su fada, Amurka tana bayan Hutu, Faransa kuma tana bayan Tutsi, rigimar yana amfanan su Yamma din ne. Suka hada su fada, wani irin fadan da a tarihi aka ce ba a taba ganin mummunan fada na kabilanci irinsa ba. Kisa, kisa kawai. Galiban wadanda aka fi kashewa su ne Tutsi din, saboda su Hutu ne suke ramuwar gayya a kan cewa su Tutsi a tarihi sun yi musu mulkin-mallaka, -sun mallake su sun wulakanta su.


Wani Bahute da aka bashi labarin yadda Tutsawa suka rika bautar da Hutawa, to uwarsa Tsutsi ce, sai ya kashe ta. Wacce ta haife shi fa ya kashe. Yace kuma ko sau nawa ta dawo duniyar nan sai ya sake kashe ta, saboda an fada masa tarihin irin wulakancin da Tutsi suka wa Hutu.


Wani kuma da me zan ce masa? Limamin coci zan ce? Saboda mu mukan yi amfani da kalmominmu ne a gare su, muna cewa liman. Su kuma ba liman suke cewa ba, wani abu ne daban. To amma dai ibararmu ne za a fi ganewa. Limamin coci ne, shi Hutu ne, sai ya tattara Tutsi da yawa a cikin cocinsa da nufin ya basu mafaka, sai ya je ya kira samarin da ke kisan kai, suka karkashe su suka cinna wa cocin wuta.


NA TABA SHAN ALWASHIN BA ZAI YIWU A YI FADA A TSAKANIN KABILUN DA SUKE MUSULMI BA


To, lokacin (da na je) ana gayan fadar. To sai a lokacin na yi magana a wajen taron, sai nake ce musu, kun ga Tutsi da Hutu din nan, da a ce Musulmi ne ba za su yi fadan Kabilanci ba. Saboda shi Musulunci yana hada mutane ne. Kun ga Aus da Khazraj suna fada da juna ne, har suna kwana da takubba tsirara saboda kowane lokaci za a iya barkewa da fada, sun shekara kusan 120 suna fada, amma da Manzon Allah (S) ya je Madina sai suka hade suka zama abu guda daya, aka manta da batun Aus da Khazraj.


 Haka kuma akwai yakin da ake ce ma Harbul Basus, tsakanin banu Bakar da banu Taglib wanda shi kuma ya shekara 150 ana yi, zuwan Manzon Allah (S) shima wannan yake-yaken nasu ya kau, aka dena bin bashin jini. Shi Musulunci yana hada mutane ne.


 Sai na basu wani misali, nace to mu a Nijeriya muna da wasu mutane da suka yi kama da Tutsi, sune Fulani makiyaya. Duk da Hutu basu yi kama da Hausawa ba, tunda su Hutu kamar yadda nace su kabila ne, amma na sha nanata cewa su fa Hausawa ba kabila bane. Duk wanda yace akwai kabilar Hausa, bai san Hausa ba.


Jawabin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Yayin Ziyarar Goron Sallah (7)


MAHUKUNTAN KASAR NAN CEWA SUKE KAR MU RAYU GABADAYA


To, mun sha fada musu, tun ma ina tsammanin a shekarar 2000 ne da aka yi wani taro aka gayyaceni na je a Kaduna. Sai wani yake tambayata cewa, Malam dangane da irin wadannan abubuwan da suke faruwa kullum a yi ta harbe-harben nan, ba yadda za a yi a kauce masa a daina wadannan harbe-harben ne? Nace to wa kaga yake harbin? Mu muke yin harbin? Ina tambayarka, mu muke harbi? Yace a’a. Nace to ka gani, wadanda suke harbi za ka yi ma magana, amma mu kace mana mene?


 Abin da suke ce mana shine kar ma ku rayu. Ko baku sani ba? Basu ce mana kar ku yi Quds ba, kar ma ku rayu (suke ce mana), domin ko a gidanka ne za a bi ka a harbe ka ne. To me ka yi kenan? Ko baku lura da wannan ba? Kar ya zama akwai ka ne kawai. Sai kace su suka yi halitta. Mahaliccinka ya halicceka ya baka ‘yanci, amma wai su basu son ganinka wai ka mutu kawai.


 To, sai kace to na fasa rayuwar? Na fasa rayuwa don ku kyaleni da raina? Ko kuwa sujada suke so mu yi musu? To ina tsammanin ko an yi musu sujada sai sun harbe mutum. Ko da za mu ce musu mun bi Allah mun bi ku. Za su ce a’a ba mu son wannan, a bi mu kawai kar a bi Allah. Kace na bi ku din. Sai sun ce maka, kace kuma baka bin Allah. Eh mana, ai ba iyaka ga abin da za su nema. Sai su yi ta neman kari. Kana bude kofa to ba iyaka.


KISSAR WASU MUMINAI DA SUKA MIKA WUYA GA AZZALUMAI


Na taba baku labarin wani kissa wanda ya auku ne da gaske a Hadisi ya zo, cewa wadanda suka gabata (ba a zamanin wannan Manzon ba), cikin Annabawan da suka gabata, (akwai lokacin da) wadansu Muminai suna fada da wadansu kafirai, a wajen yakin sai aka kama wasu Muminai, aka kulle su ana azabta su a gidan yari. To, sai wazirin garin yace, maimakon azabtasu da muke yin nan, mu basu mukamai ne, sai su bi mu. Mu ce musu kowannensu za a bashi gari guda a matsayin gwamna (ko Amir), sai su daina wannan abin da suke yi din, ka ga sai mu yi galaba a kansu.


 Sai aka je aka ce musu to, yanzu abin da muke so da ku, a maimakon azabar da kuke sha din nan, idan kuka yarda kuka bi mu, to shikenan za mu baku ma sarauta, kowanenku za a bashi gari guda, shikenan kun ga kun huta. Sai wasu suka ce, to ai mun samu mafita, idan aka bamu sarauta ba sai mu sulale mu gudu ba? Kaga mun samu mafita, yanzu da za a bamu gari mu yi sarauta kaga sai mu samu mu gudu. Suka ce wannan dabara ne. To sai wasu suka ce to mun yarda, wasu kuma suka ce mu bamu yarda ba. Sun rabu biyu kenan, wasu suka yarda.


 Wadanda suka yardan sai aka zo da su, aka ce to ku kun yarda? Suka ce eh. Kowane za a bashi gari ya zama Amir, kuma ya daina wannan abin, yanzu zai bi mu ne? suka ce eh. To shikenan, sai waziri yace, to amma idan muka yarda muka ce musu mun basu sarauta alhali suna cikin addininsu ba a addininmu ba, yaya kenan? Ai ba za mu amince musu ba. Sai aka ce, ace su fita daga addininsu ne.


 Su fa Muminai ne, amma sai aka ce musu to yanzu in dai za mu amince muku sai dai idan kun bar addininku. Wadannan mutanen suka ce to fa, ka ga wata fitinar kuma fa! Muna fata a bamu sarauta mu sulale, yanzu kuma a ce sai mun bar addinin? Mene abin yi? Wasu suka ce mu bari kawai sai mu ce mun bar addinin, idan muka gudu sai mu koma ga addininmu. Sai suka ce to shikenan mun fita addinin namu. Shikenan sai suka fita addininsu, wato ma’ana yanzu su ba Musulmi ne ba.


 Sai waziri yace, a’a, to sun fita daga addininsu to amma basu shiga namu ba ai, ya za mu amince musu? Ba za mu amince musu ba. Sai suka ce musu to mun ji kun bar addininku, wannan yana da kyau, amma yanzu baku shiga namu ba ai, sai ku shiga namu. Su kuma nasu bautar gunki ne.


 Sai mutanen suka ce kai kaga wata fitina, yanzu idan muka ce mu shiga addininsu yanzu kuma mun halaka. Yanzu to yaya kenan? Wane yanzu meye abin yi? Suka ce to mu shiga addinin nasu, idan muka samu suka bamu wannan mukamin, kaga sai mu gudu mu koma namu. Sai suka zo suka ce shikenan, mun shiga addinin naku. Ka san kuma za a ce su je su yi bauta ko? 


 To bayan nan suka ce, to gashi kun bar addininku kun shiga namu. Inji waziri. Yace amma kuma idan mutanensu suka zo suna yakarmu ai za su goyi bayan mutanensu ne, ya muka tabbatar da cewa mu za su goyawa baya? Akace eh kuwa fa, to mene abin yi? Yace ace su kashe wadancan ‘yan uwan nasu da suke kurkuku wadanda basu yarda ba. Su je su kashe su, sannan mu tabbatar suna tare da mu dari bisa dari. 


 Aka ce yanzu sai ku je ku kashe wadancan sauran mutanen da kuka bar addininsu kuka shiga namu, su suka ki suka tsaya a kan addininku na da. Sai ku je ku kashe su, mun san cewa kuna tare da mu kenan. Suka ce kai! Wannan al’amari kuma? Idan muka ce ba za mu kashe su ba kuma za a kashe mu ne. Sai suka je suka karkashe su. Ah to, ba Taqiyya ba kuma dai? 


Da suka je suka kashe ‘yan uwansu, sai waziri yace kai-kai-kai, tunda suka kashe ‘yan’uwansu to mu ne ‘aula’ da su kashe mu, saboda haka mu kashe su. Sai aka kashe su.


Wannan ba tatsuniya bace, ya auku ne don Hadisi ne ya zo da shi. A wadanda suka gabata (ya faru), lokacin Annabawan da, ba a lokacin Manzon nan ba. Wannan yana nuna maka cewa su babu iyaka ga abin da za su nema, gara kai ka bude kofa tun asali. Idan ka yi wannan za su ce maka ai bai isa ba, idan ka yi wannan sai wannan kuma.


Za mu cigaba.