Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

13 Mayu 2023

16:52:18
1365391

Al'ummar Yaman Sun Tsaya Tsayin Daka Da Gwagwarmayar Palasdinawa

Shugaban Majalisar Hadin Kan Kabilanci a kasar Yaman, Daifallah Rassam, ya tabbatar da hadin kan kabilun kasar Yemen tare da tsayin dakan Palastinawa wajen tunkarar Yahudawan da daukar fansa kan mamayarsu yana mai jaddada cewa batun Palastinu shi ne batu na farko kuma na tsakiya na kasar Yemen.

 Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, shugaban majalisar hadin kan kabilu a kasar Yemen Dhaifallah Rassam ya tabbatar da hadin kan kabilun kasar Yemen tare da goyawa Palastinawa baya wajen tinkarar da kuma daukar fansa kan al'ummarsu akan Yahudawan mamaya, yana mai jaddada cewa batun Palastinu shi ne batu na farko kuma na tsakiya na kasar Yemen. 


Rassam ya yi kira ga shugabannin siyasa da su bude kofar jihadi da bude sansanonin daukar da kuma horar da kabilun kasar Yemen.

Har ila yau, Rassam ya tabbatar da cewa kabilu 92 sun ba da sanarwar gudummuwarsu tare da mayaƙa 5,000, "suna kira ga tsarin gwagwarmaya ga daidaikun mutane, kabilu, gwamnatoci, da ƙasashe da su kasance cikin shiri."

Rassam ya yi gargadi game da toshe hanyoyin kabilar Yaman, yana mai nuni da cewa duk wanda ya tsaya kan hanyarsu, "zai kasance dan Isra'ila kuma zai kasance makiyin kabilun Yemen."

Wannan sanarwar ta zo ne a wani taron kabilanci da aka gudanar a birnin San'a na karrama kungiyar Jihad Islami, a taron wakilin kungiyar Jihad Ahmed Baraka ya bayyana cewa, kabilun kasar Yemen su ne a sahun gaba wajen bayar da goyon baya ga dukkanin dalilai na adalcin al'ummar, wanda mafi yawansu shi ne batun Falasdinu.

Hakazalika, Baraka ya kara da cewa "ba don goyon bayan gwamnatocin da suka ci amanar Larabawa ba, da Yahudawa ba za su iya ci gaba da zama a Falasdinu ba."


A kwanakin baya, shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar Yemen Mahdi Al-Mashat, ya tabbatar da goyon bayan kasar Yemen, da shugabancinta, da gwamnati, da al'ummar kasar, dangane da dukkanin zabin da jagorancin gwagwarmayar Palastinawa suka dauka na dakile makiya 'yan sahayoniya," suna kira ga kasashen Larabawa da na Musulunci da su dauki matsayi da mataki don tallafawa al'ummar Palastinu da gwagwarmayarsu da kuma tallafa musu da kudi da makamai." Kauracewa kayayyakin Amurka da Isra'ila.

A rana ta biyar a jere dakarun haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kai hare-haren soji kan zirin Gaza, yayin da jiragen yakin mamaya suka kai hari kan gidaje da wurare a arewaci da tsakiya da kuma kudancin yankin na zirin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.

Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza ya kai 33, ciki har da yara 6 da mata 3, yayin da wasu 147 suka jikkata.

Kisan gillar da Isra'ila ke ci gaba da yi wa jagororin gwagwarmayar Palasdinawa, wanda na karshe a jiya Juma'a ne, a lokacin da dakarun Quds Brigades, bangaren soji na kungiyar Jihadi Islami suka sanar da shahadar wani mamba na majalisar soji da kuma jami'in sashin ayyuka, Iyad Al-Hassani, "Abu Anas", bayan da jiragen saman mamaya suka kai hari a gidansa da ke unguwar Al-Nasr, a cikin garin Gaza.

Baya ga shahidi al-Hassani, dakarun na Quds sun yi jimamin jagororinsu 5 da suka yi shahada tun farkon hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza. Kuma "Jihadin Musulunci" ta sha alwashin cewa "laifi na kashe shugabannin rundunonin Kudus zata wanzarwa makiya da firgita da fatattakar tsaronta da sojojinta."