Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Mayu 2023

22:30:56
1364271

Sharuddan Lafiya Da Alluran Rigakafin Da Saudiyya Ta Amince Da Su Don Aikin Hajji

Saudiyya Ta Sanya Sharuddan Lafiya Da Alluran Rigakafin Da Ta Amince Da Su Don Aikin Hajji


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Ma'aikatar lafiya ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, dole ne wadanda ke da niyyar zuwa aikin Hajjin bana su samu yin allurar rigafin ciwon sankarau, mura na yanayi da sabbin alluran rigakafin cutar corona.


Ma'aikatar da aka ambata ta jaddada cewa: Wadanda ba su yi allurar rigakafin mura na yanayi ba ya kamata su dauki matakin samun wannan rigakafin da wuri-wuri. Ya kamata a yi allurar wadannan alluran daga yanzu zuwa kwanaki 10 kafin fara aikin Hajji.