Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Talata

9 Mayu 2023

22:24:38
1364269

Hamas: Gwamnatin Yahudawan Sahyoniya Za Ta Dandani Sakamako Kan Laifukan Da Ta Aikata A Zirin Gaza

A cikin wata sanarwa da suka fitar na ta'aziyyar shahadar Jihad Shakir al-Ghanam, Khalil Salah al-Bahtini, da Tariq Muhammad Ezzeddin, kwamandojin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, da wasu 'yan kasar Falasdinu a Zirin Gaza, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa,

A cikin wata sanarwa da suka fitar na ta'aziyyar shahadar Jihad Shakir al-Ghanam, Khalil Salah al-Bahtini, da Tariq Muhammad Ezzeddin, kwamandojin kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinu, da wasu 'yan kasar Falasdinu a Zirin Gaza, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara. Kungiyar Hamas ta jaddada cewa gwamnatin sahyoniyawan za ta dandani Sakamakon laifukan da ta aikata.A cikin wannan bayani, yayin da ake ishara da wuce gona da irin da gwamnatin sahyoniyawan ta yi a yankin Zirin Gaza, an jaddada cewa, cikakken alhakin wannan aika-aika na dabbanci da sakamakonsa yana kan gwamnatin sahyoniyawa da majalisar ministocinta fasikai masu tsattsauran ra'ayi.