Bismillahir Rahamanir Raheem.
Wasallallahu Ala Sayyidina Wa Nabiyina wa Habibi Qulubina Abul Qasimi Mustapha Muhammad wa ala alihid Dayyibinad Dahirinal Ma’asumiyn.
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi Ta’ala wa barakatuh.
Yau Laraba 21 ga watan Ramadan, hijira 1444. To, zan dauki wadannan mintoci ne na tunatar da mu cewa, yau fa ranar Shahadar Amirulmuminin (AS) ne. Wanda aka sara ranar 19 ga watan Ramadan, ruhinsa tsarkakka ya bar gangan jikinsa a yammacin 21 ga watan Ramadan. Saboda haka muna taya al’umma jaje. Muna cewa Aazamallahu ujurana bi musabina bi Amirulmuminin (AS).
Kuma a gabanmu, jibi Juma’a akwai ranar Quds na duniya, wanda akan nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu kan ta’asar da ake musu a mamayar da aka musu. To kuma na bana, ya zama ya fita daban da na sauran shekaru. Saboda tun kamawar Rajab, mutanen nan (isra’iliyawa) sai sun yi kisan kai. Kullum sai an kashe Bapalasdine. Wannan al’amari yana da ban-al’ajabi. Kuma da Ramadan ya kama sai aka shiga tsanantawa, yanzu Masjidul Aqsa ne za su je su tarwatsa masu sallah, basu damu ba su kakkama mutane su daddaure. Hotuna na iya nunawa idan mutane sun damu da su gani.
To, a bara mun karfafa guiwar mutane a kan nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar Palasdinu. Akwai wani abu da ake yayin cewa a rika daga tutar Palasdinu, suna cewa; #FlyThePalasdinianFlag. To kuma Alhamudulillahi, ‘yan uwa a muzaharorinsu a nan Abuja duk su kan rika daga tutar Palasdinu ko da ma muzaharar suna yi a kan wani abu ne, ranakun Litini da ranar Juma’a da wasu raneku da su kan yi Muzaharori, duk suna rika daga tutoci. Saboda haka yana da kyau a daidai wannan lokaci a rika daga wadannan tutoci na nuna cewa muna tare da al’ummar Palasdinu.
Nuna muna tare da al’ummar Palasdinu nuna muna tare da wani abu ne da ya dame mu duk cikarmu, domin Palasdinawan nan da ake ta faman kashewa, a madadinmu suke wannan gwagwarmaya, - a madadin dukkan al’ummar Musulmi ne. Domin kuwa wadanda suke musu abin da suke musu, idan suna iyawa, to za su yi ma kowa da kowa. Kuma basu ma boye ba, akwai wani makiyin Allah makiyin Annabi (S), wanda yake cewa wai yakin duniya na uku, duk wanda ma bai ce yana nan tafe ba, kamar bai san abin da yake yi bane. Wai yana nan tafe. Kuma a lokacin yace, za su kona Musulmi. Za su kona Larabawa. Bai ko boye ba. Yace, za su kona su ne kurmus. Haka yace.
Kila za ku san shi, baro-baro yake wannan maganar. Saboda haka su abin da suke tunani shine, su za su yi fada ne da al’ummar Musulmi gaba daya. Kuma hankoronsu ba Palasdinu ne kawai ba, za su kafa daular isra’ila ce da za ta mamaye dukkanin wannan yankunan, wanda ya hada kasashen Palasdinu, da Urdu, da Syria da Arewacin kasar da ake ce ma Saudi Arabiyya, har da Birnin Madina.
Su a wajensu wai suna cewa wai Birnin Madina ma wai birninsu ne, wai da Yahudawa ne a wajen kafin wai Annabi (S) ya je ya kore su. Ko da yake ba Annabi suke ce masa ba. Wai ya je ya kore su. Kamar yadda suke cewa wai ya karkashe su ya kore su a kasar, wai kasarsu ce. Saboda haka sun zana taswira wanda suka saka Madina a ciki, su a wajensu za su mamaye wannan wajen ne, kuma tunaninsu kenan. Insha Allahu wannan mafarki nasu ba zai taba yiwuwa ba. Amma kuma dai mafarki ne kuma suna ta ta’asarsu.
Saboda haka, ya kamata duk al’ummar Musulmi su nuna damuwarsu. A yi shirin wannan Ranar Quds, a yi ta a ko ina. Mun san cewa da mun zabi wadansu birane ne musamman muka ce a nan ne za a yi Quds, da kamar birni 22 muke yi, to amma saboda irin yanayin tsaro da aka jefa kasar nan a ciki, wanda tafiye-tafiye ma da wahala, saboda haka sai ya zama wadansu birane ma da ba a saba yi ba duk an yi bara, bana ma haka nan. Saboda haka za a iya yi a biranen da ma ba a saba yi ba. In zai yiwu, yana da kyau a je a yi a manyan birane, in ma ba zai yiwu ba, wadansu biranen da ba a saba yi ba ma du kana iya yi. Ba kamar Ashura da muka ce ko a kauyuka za a iya yi ba, ita ranar Quds ranar ‘Tadamun’ ne, kamata ya yi ita duniyar ta gani muna tare da su, (don haka) za a yi a muhimman wurare.
Ba kuma kawai ranar Quds ne za mu nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar Palasdinu ba, duk wannan lokacin da ake musu wannan ta’asar ya kamata mu nuna, tunda sauran duniya ma suna yi. Idan mutum yana bibiyan labaru zai ga a sauran biranen duniya, duk an ta fitowa ana nuna rashin goyon baya ga irin ta’asar da ake ma al’ummar Palasdinu a wannan wata mai tsarki na Ramadan. Saboda haka bai Kaman a ce mu sai ranar Quds din ne kawai za mu yi ba, a kowane lokaci ma ya kamata ya zama muna nuna ‘tadamun’, a zantukanmu da kalamanmu da rubuce-rubucenmu a jaridu, da kuma shafuffuka na yanzu (da ake) zamanin ‘internet’, da kuma wakoki da ire-irensu, duk a rika tunatar da al’umma, a fadakar da ita kan abin da ke faruwa a al’ummar Palasdinu, ya zama ya shafe mu gaba dayanmu.
Ina fatan mu ga sauyi insha Allahu. Kuma sauran al’umma da suke kallon abin na wasu ne, to muna fatan Allah Ya fadakar da su, su gane cewa na kowa da kowa ne.
Wasallallahu ala Muhammadin wa ala alihid Dahirin.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Ta’ala wa barakatuhu.
- Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar da wannan jawabin ne ranar Laraba 21 ga Ramadan, 1444 (12/4/2023) a gidansa da ke Abuja, inda aka yada ta kafafen sadarwa. Cibiyar Wallafa ta rubuto daga bidiyon.

