Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

3 Afirilu 2023

21:17:50
1355936

Jami'an Tsaron Najeriya Sun Bude Wuta Ga Magoya Bayan Sheikh Zakzaky A Abuja

An harbe magoya bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky a babban birnin Najeriya.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (A.S) ABNA ya ruwaito - Sojojin Najeriya sun yi luguden wuta kan taron magoya bayan Shaikh Ibrahim Zakzaky, jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, a Abuja, babban birnin kasar nan.

Gungun mabiyan da suke neman sakin Fasfo na shugaban nasu da Hukumar Najeriya ta rike.


Sakamakon harba-harben da aka yi ma magoya bayan Shaikh Zakzaky da dama sun samu raunuka, kuma an kai su asibitocin Abuja domin yi musu magani.


Magoya bayan Shaikh Zakzaky sun bukaci a saki fasfo din wannan malamin Shi'a na Najeriya tare da matarsa ​​a watia muzaharar da suka yi a Abuja, a lokacin ne aka bisu da harbi.


Sun yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta baiwa shugaban nasu cikakken 'yanci ta hanyar sakin fasfo dinsa domin ya fita kasar waje domin duba lafiyarsa.


Shaikh Zakzaky na fama da munanan rashin lafiya sakamakon harbin bindiga da jami’an tsaro suka kai masa a gidansa a shekarar 2015, wanda ba a iya jinyarsa a Najeriya.


A shekarar 2021 ne kotun kolin jihar Kaduna ta Najeriya bayan shafe shekaru shida a gidan yari na tsare Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa, ta wanke jagoran Harkar Musulunci na kasar nan, tare da sake shi bayan shafe shekaru yana tsare a gidan yari. Amma sai ya zamo Fasfo din Shaikh Zakzaky da matarsa ​​har yanzu ba a ba su ba.


An kama Shaikh Zakzaky da matarsa ​​da daya daga cikin 'ya'yansu a watan Disambar 2015 a lokacin da sojojin Najeriya da 'yan sanda suka kai hari a gidansa da Husainiyya da ke garin "Zaria" a lardin "Kaduna" na Najeriya. 

Yayin gudanar da wannan harin, kimanin ‘yan Shi’ar Nijeriya 2,000 ne suka yi shahada, uku daga cikinsu ‘ya’yan Shaikh Zakzaky ne. Jami’an ‘yan sandan kasar nan sun harbe wasu ‘ya’yan uku na jagoran Harkar Musulunci a Najeriya shekara guda da ta wuce a yayin bikin ranar Qudus ta duniya a shekarar 2014.


Bayan harin da sojoji da jami'an tsaron gwamnatin Najeriya suka kai wa "Husseinya Baqiyatullah" (AS) Sheikh Ibrahim Zakzaky ya samu munanan raunuka, sakamakon tsananin raunukan da ya samu, ya rasa idonsa daya gaba daya, sannan idonsa na kan daya yana da damuwa bakin.

Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya ya sha fama da hawan jini a lokacin da yake tsare a gidan yari.


Haka kuma, da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa sun yi tir da kisan ‘yan Shi’ar Najeriya da ‘yan sanda da jami’an tsaro suka yi a Abuja. Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta rawaito cewa sojojin Najeriya da jami’an tsaron kasar sun aikata kisan ‘yan Shi’a tare da binne su a kaburbura na baidaya da kuma lalata wasu takardu masu alaka da wannan laifi.