Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

25 Maris 2023

19:18:52
1354147

Mutane Da Dama Sun Rasa Rayukansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Somaliya

Tashar talabijin ta Somaliya ta bayar da rahoton cewa, gidaje da dama ne ambaliyar ruwa ta mamaye, kuma ta shafe filayen noma da ke yankin...

Tashar talabijin ta Somaliya ta bayar da rahoton cewa, gidaje da dama ne ambaliyar ruwa ta mamaye, kuma ta shafe filayen noma da ke yankin...


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul Biyt As ABNA ya habarto cewa, kimanin mutane 20 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye yankunan Bartiri na jihar Gedo a kudancin kasar Somaliya.


Tashar talabijin ta kasar Somaliya ta bayar da rahoton cewa, ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje da dama tare da shafe filayen noma a yankin, inda ya ce a halin yanzu gwamnati da kawayenta na kasa da kasa suna aikin tantance irin barnar da aka yi da kuma kokarin kai agajin gaggawa ga wadanda lamarin ya shafa.


A nasu bangaren mahukuntan birnin Bartiri sun ce: Ambaliyar ruwan da ruwan kogin Juba ya haddasa ya mamaye yankuna da dama a cikin birnin, kuma dubban mutane sun rasa matsugunansu daga kauyukan da ke gabar kogin.


Wani abin lura shi ne yadda aka fara samun ruwan sama a kasar Somaliya a yawancin sassan kasar, a daidai lokacin da mutane ke fuskantar matsanancin fari a shekarar da ta gabata, wanda a cewar wani rahoton MDD, ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 43,000 a kasar Somaliya. sakamakon fari mafi dadewa a kasar, kuma rabinsu akwai yiwuwar Kasancewarsu yara ne.