Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

20 Maris 2023

13:22:55
1353135

An gudanar Da Taron Koli Na Majalisar Ahlul-baiti As Ta Duniya A Iraki

Majalisar Koli Ta Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya Tayi Kira Da A Kara Wayar Da Kan Al’umman Duniya Domin Kare Alfarma Wurare Masu Tsarki

A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Ahl-Bait- As Abna, an gudanar da taron majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Bait As a birnin Bagadaza tare da halartar mambobin majalisar daga kasashe daban-daban na duniya kuma Hujjat Il-Islam Sayyed Ammar Hakim daya daga cikin mambobin majalisar koli ta majalisar ne ya karbi bakuncinsu

An gudanar Da Taron Koli Na Majalisar Ahlul-baiti As Ta Duniya A Iraki


A cewar wakilin kamfanin dillancin labarai na Ahl-Bait- As Abna, an gudanar da taron majalisar koli ta majalisar duniya ta Ahlul-Bait As a birnin Bagadaza tare da halartar mambobin majalisar daga kasashe daban-daban na duniya kuma Hujjat Il-Islam Sayyed Ammar Hakim daya daga cikin mambobin majalisar koli ta majalisar ne ya karbi bakuncinsu.


  Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-baiti (AS) ta Duniya a yayin da yake gabatar da rahoto kan nasarorin da majalisar ta cimma da kuma matakan kawo sauyi, ya bayyana cewa: Majalisar Ahlul Baiti ta duniya tana goyon bayan hakkokin 'yan shi'a daban-daban a sassan duniya.


Har ila yau, Ayatullah Akhtari, shugaban majalisar koli ta majalisar Ahlul-Baiti (AS) ya bayyana cewa: A cikin tarukan majalisar koli na majalisar, an mai da hankali kan matsaloli da batutuwa daban-daban na duniyar musulmi.


  Wannan taro dai ya kare ne da fitar da Bayanin da a cikinsa ya kunshi bayanin da kiran mambobin majalisar koli ta Ahlul-baiti As da a kara wayar da kan al’ummar musulmi da kuma mabiya tafarkin Ahlul Baiti (AS) wajen kare abubuwa da wurare masu tsarki.