Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA
Asabar

14 Janairu 2023

21:02:39
1338471

MAULIDIN SAYYIDA ZAHRA (SA) A ABUJA

Har Abada Ba Zamu Taɓa Sallamawa Azzalumai Ba

Tattaunawar ta biyo bayan dawowa daga hutun sallah da cin abinci da akayi ne. Daga bisani kuma sai jawabin rufewa daga Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda ya gabatar a yayin ziyarar yan uwa mata da suka kai mishi a gidansa dake Abuja.

Jim kadan da kammala jawabin Malama Zeenah wurin taron maulidin Sayyida Zahra (SA) a Abuja yau Asabar rana ta Biyu. An gabatar da tattaunawa kan darussan da za’a dauka daga rayuwar Sayyida Zahra (SA).


Tattaunawar ta biyo bayan dawowa daga hutun sallah da cin abinci da akayi ne. Daga bisani kuma sai jawabin rufewa daga Shaikh Ibraheem Zakzaky wanda ya gabatar a yayin ziyarar yan uwa mata da suka kai mishi a gidansa dake Abuja.

Raba kyaututtuka ya yaran da sukazo na Daya dana Biyu ya biyo bayan sauraron jawabin rufewa daga Jagora (H), sai kuma yanka cake alkakin Maulidin Sayyida Zahra dana jikanta Imam Khomaini (QS), sai kuma addu’an tashi. Wannan shine ya kawo karshen taron rana ta Biyu.

Uwar Gidan Sheikh Zakzaky Ta Sake Jaddada Cewa, “Har Abada Ba Zamu Taɓa Sallamawa Azzalumai Ba”


A ƙarshe ƙarshen jawabin da uwar gidan Sheikh Zakzaky Malama Zeenat Ibrahim ta gabatar Yau a gurin bukin Maulidin Sayyida Zahara (s.a) a Abuja, ta sake bayyana cewa “har abada ba zamu taɓa miƙa wuya ga azzalumai ba” wannan zancen na zuwa ne a daidai lokacin da take bayani akan waɗansu maganganu da ake yawo dasu cewa, “Sheikh Zakzaky da gwamnati sun yi yarjejeniya kan cewa ya daina gwagwarmayar tabbatar da addini da yake yi shekara da shekaru”.

Malamar ta cigaba da cewa, “ Yau ina da shekaru 65 a duniya kuma tun ina da shekaru 16 nake wannan gwagwarmaya haka Malam tun yana da shekaru Ashirin da... Yake wannan harka, duk daɗin duniya Ni ban san dashi ba wahala na sani, to duk waɗannan shekarun da aka shafe ana wannan sai yanzu da rana tsaka sai mu sallamawa azzalumai ? Mu kalli waɗanda aka karkashe a wannan Harka me”.

A ƙarshe Malama Zeenat ta ƙarƙare da miƙa saƙo ga azzalumai cewa, “idan ma har dagaske ne yarjejeniya aka yi to mun take yarjejeniyar, ballantana ma ba wata yarjejeniya da aka yi da wani, tabbas sun taɓa neman Mu da wannan maganar ta cewa a yi yarjejeniya dasu amma Malam sai ya ce musu “Mun san Muna Fama Da Rashin Lafiya Mun San Kuma Wannan Rashin Lafiyar da Muke Ko da Wane Lokaci Allah Zai Iya Ɗaukar Ranmu Amma Ƙara Mu Mutu Da Mu Sallama Muku” a sharaɗin da suka bamu sun ce zasu bar mu mu fita neman lafiyars amma Malam ya gaya musu "Sam! Ba Zai Taɓa Ɗaukar Walaƙanci Ba." 

14/1/2023.