Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

28 Disamba 2022

10:37:50
1333984

Tunawa da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan Shi'a a Zariya Najeriya 2015

A shekarar 2015 ne sojojin Najeriya suka kashe daruruwan mutane ta hanyar kai wa 'yan Shi'ar kasar hari a yankin Zaria.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (AS) - Abna - ya ruwaito A kwanakin baya ne ‘yan Najeriya suka fito kan tituna domin tunawa da cika shekaru 7 da kisan kiyashin da aka yi a Zariya a shekarar 2015 a Abuja da manyan biranen kasar.Muzaharar dai na dauke da tutoci da kwalaye masu dauke da hotunan Sheikh Ibrahim Zakzaky shugaban Yan Shi'a a Najeriya.Mahalarta wannan taruka na tunawa waki'ar na dauke da wasu sakonni da suka shafi kisan gillar da aka yi a "Zaria" a tarihi.


Bayanin abin da ya faru a kisan kiyashin ZariyaWannan laifin ya faru ne a shekarar 2015 a kuma ranar 12-14 ga watan Disamba (Azer 1394) a garin Zaria a jihar Kaduna.Wani bincike na jama'a ya zargi sojojin Najeriya da kashe 'yan Shi'a 347 tare da binne su a wani kabari da aka yi a garin Kaduna da ke arewacin kasar a karshen shekarar 2015.Rikicin na kwanaki biyu ya fara ne a ranar 12 ga watan Disamba lokacin da sojojin Najeriya suka far wa mabiya Shi'a a wani taron bikin addini da kakkausan kisa wanda suka ce sunyi hakan ne don yan shian sunyi nufin hana ayarin sojoji wucewa.Rahoton mai shafuka 193 ya ce sojojin Najeriya sun yi amfani da karfin tuwo ne akan yan shian inda Mutane 349 ne suka rasa rayukansu a wannan harin.


’ya’yan Shaikh Zakzaky 3 ne kuma suka yi shahada a wannan kisan kiyashi.Rushe gidajen 'yan Shi'a, kamawa da tsare da yawansu, kona fararen hula da ransu, tona kaburbura, kashe yara 193, kisan kiyashin da aka yi wa mata 297 ciki har da mata masu juna biyu 23, da sauransu. Najeriya a watan Disamba 2015.Har yanzu ba a yi adalci ba
Kungiyar Shi’a a Najeriya ta sha yin kira da a yi adalci ga daruruwan mutanen da sojojin Najeriya suka kashe a watan Disamban 2015.
Sai dai ya zuwa yanzu babu wani martani dangane da wannan batu kuma hukumomin kasa da kasa ma sun yi shiru kan wannan batu.Bakin ciki mara iyaka bayan kisan da aka yi a ZariyaSafiya Umar matar daya daga cikin wadanda suka yi shahada a wannan lamari, ta ce: Ina ma ace na ji karshen maganar mijina kafin shahadarsa. Ba su ma bari mu ga jikinsu ba; Dukkansu an binne su ne a wani kabari da ban sani ba sai yanzu.Kamar "Safiya Umar", itama "Maimuna Munkailah", mai shekaru 40 zuwa 45, ta ba da labarin bakin ciki irin wannan; A cewarta, kawai an sanar da ita cewa mijinta ​​ya yi shahada a wannan kisan kiyashi.Tana cewa: Mijina da wasu mutane uku sojoji sun harbe su a lokacin da suke barci a kasa kuma suka yi shahada.Sojojin Najeriya na harbe 'yan Shi'ar Najeriya ba tare da hakkinsu ba sai da da zimmar wasu dalilai, kamar halartar muzaharar lumana ta neman a sako Shaikh Zakzaky; Har ila yau, an bayyana ayyukan kungiyar Shi'a ta Najeriya a matsayin haramtacciya bisa karya da zalunci.