Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Jummaʼa

2 Disamba 2022

20:01:31
1328002

Suna adawa da ni saboda ni musulma ce

Yar Majalisa Wakilan Amurka Musulma daga jam’iyyar Democrat ta yi kakkausar suka ga shugabannin Jam’iyyar Republican inda ta bayyana cewa matsayar da suke dauka kanta saboda kasancewarta Musulma ce.

Kamfanin dillancin labaran ABNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, Ilhan Omar, wakiliya ‘yar asalin kasar Somaliya a majalisar dokokin Amurka, ta sake sukar Kevin McCarthy, wanda ake sa ran zai sake zama shugaban majalisar wakilan Amurka, da kuma kalaman da yake yi kanta na batunci.

A nasa jawabin McCarthy ya ce idan ya zama shugaban majalisar a watan Janairu, zai cire Ilhan Omar daga zama mamba a kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar.

McCarthy ya saka wani faifan bidiyo na jawabinsa a taron shekara-shekara na kungiyar hadin kan Yahudawa ta Republican, wanda aka gudanar kwanaki kadan da suka gabata, a shafinsa na Twitter cewa: Na sake yin wani alkawari kuma yanzu na sake maimaita cewa zan cika wannan alkawari, game da Ilhan Omar, wakiliyar kungiyar IS.

Bayan fitar da wadannan kalamai, Ilhan Omar ta mayarwa McCarthy da martani a shafinta na Twitter inda ta rubuta game da McCarthy da masu ra'ayinsa cewa: Wadannan su ne mutanen da suka yi ikirarin cewa Obama musulmi ne wanda aka haife shi a Kenya kuma bai kamata ya rike mukamin shugaban kasa ba

Waɗannan su ne mutanen da suke ganin rantsuwa da kur'ani daidai yake da dakatar da su daga halartar Majalisa. Waɗannan su ne mutanen da suka yi mini adawa tun ranar farko a cikin kwamitin kula da harkokin waje, kuma suka ce a matsayina na musulma ba zan iya samun damar sanin sirrin Amurka ba. Waɗannan su ne mutanen da suke kiran mu masu kishin Islama idan muna magana game da take haƙƙin ɗan adam.


342/