Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (A.S) ABNA ya habarta cewa, kafar yada labaran Falasdinu ta bayar da rahoton cewa, an kashe wata yarinya Bafalasdine sakamakon harbin da aka sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka yi mata a garin Bitonia da ke yammacin Ramallah a yammacin kogin Jordan.
Bisa labarin da aka samu na farko, sojojin Isra'ila sun harbi wata motar Falasdinawa tare da fasinjoji biyu a wannan birni.
Wannan yarinya Bafalasdiniya ce mai shekaru 19 sunanta Sana Attal.
Tun da sanyin safiyar jiyan ne sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kamar yadda suka saba, suka kai hari a yankuna da dama a yammacin gabar kogin Jordan da suka hada da Jenin da Nablus tare da kame wasu Falasdinawa.