Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

19 Oktoba 2022

03:58:18
1315128

Jan Kunne Ga Kafofin Yada Labaran Saudiya

Babban Kwamandan IRGC Ya Gargadi Hukumar Al-Saud

Yayin da yake ishara da barnar da kafafen yada labarai da ke da alaka da Saudiyya suke yi, babban kwamandan rundunar IRGC ya gargadi Al-Saud da cewa: Ku yi hattara da halayenku, ku kula da kafafen yada labaranku. In ba haka ba, kaikai zai koma kan mashekiya. Amma duk da haka Za mu karkare kafa maku hujja.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) ABNA ya habarta cewa, babban kwamandan rundunar sojin kasar Manjo Janar Husaini Salami, a wani jawabi da ya yi wa dakarun da ke halartar atisayen ya bayyana cewa: “Na yi matukar farin ciki da murna da cewa a yau a cikin wannan gagarumin aikin dake gudana a kasar Azabaijan wacce take mahaifar manyan malamai maza da mata maau Imani nayi Farincikin kasance wata a cikin wannan kasa.


 


 Azerbaijan Kasa Ce Ta Manyan MujahidaI


 


Ya kara da cewa: Kasar Azabaijan kasa ce ta manyan mujahidai, shahidai madawwama a cikin dakaru kuma sararin sama mai cike da daraja da taurarin shahidan al'ummar musulmi, kasar shahidan samari da Yammata dake bayyanar da kamshi da kyawawa. kasar shahidan da suka kwanta a wannan kasa, ya ku al’ummar wannan kasa.” Kuma al’umma ku zamo tabbatacciyar Al'umma da za ta dawwama a raye da alfahari.


 


Ku Ne Jigo Mai Ƙarfi Na Tsaron Al'umma Da Adon lardin


 


Babban kwamandan rundunar yayi nuni da cewa: Wannan tafarki mai ƙarfi da muke gani a yau ya nuna cewa matakan suna da ƙarfi kuma zukata suna cike da bangaskiya kuma zukata suna mika wuya. Lokacin da muka ga wannan runduna guda ɗaya, matasa kuma cike da ruhi, sai na tuna ainihin alkawuran da Allah Ta’ala ya yi a cikin Alkur’ani mai girma. Kune siffar ayoyin Alqur'ani kuma siffar hikimar Ubangiji don jin daɗin musulmi. Ku ne kagara mai ƙarfi na tsaron al'umma da adon lardin. Matukar kuna da kagara mai karfi, kuna tafiya a kasa, babu wani makiyi da zai iya taka kafarsa a kan tituna da lungunan kasarmu. Ku ƙwararrun maza ne kuma kun ga filin Gwagwarmaya kuma kuna kare lafiyar mutane da jin daɗinsu da daddare idanunku a buɗe. Duk wanda yake son yaga fuskar matasan wannan al'umma masu karfin dabaru, ya dubi fuskar wadannan matasan.


A yau, IRGC Ta Zamo Mai Karfi Sosai


 


Manjo Janar ya jaddada cewa: "An buge ku da manyan makiya." In ba don ku ba, da sun mamaye kasar nan, sun wawashe al’ummarmu tsare mai tsarki, amma makiya sun mika wuya ga karfinku da imaninku, kuma a yau kun zamo sojoji masu babban karfi.


 


Za ku kai ga duk wani makiyin da ya ke da nufin makirci kuma yana cikin gida ku buge shi ku kawar da duk wata mugun nufi. Ba don ku ba, da al'amarin takfiri ya yadu kuma ku ne kuka karya bayan takfiri, kuma ku ne kirazanku suka zama katangar wannan al'umma da ba za a taba tabawa ba.


 


An ci nasara akan abokan gaba a bayyane amma suna kutse cikin sararin samaniya


 


Ya kara da cewa: Ku ne kuka sa makiya suka cire tunanin harin soji daga zuciyarsu. Kun kori mafarkin abokan gaba har makabarta. Idan makiya suka koma kutsawa ta sararin samaniyar kafafen yada labarai, don sun gaza da ku ne a zahiri, suna yin Hakane da nufin nisantar da matasa daga juyin juya hali da asali da tarihin kasar. Matasan mu sun mayar da martani ta hanyar watsi da hayaniyar makiya. Waɗanda aka yaudare za su gane cewa waɗanda suke ganin su abokansu ne abokan gābansu ne.


 


Mun Kara Karfi Bayan Kowace Matsala


 


Manjo Janar Salami ya ci gaba da cewa: Amurka wacce ta shiga cikin al'amuran kasarmu kai tsaye, ita ce ta sanya wa al'ummar kasar takunkumin magunguna da abinci da kuma tilasta wa duniya takunkumi. A duk lokacin da Amurkawa suka zo kasar nan, mun fuskanci irin wulakancin da suka kawo wa al’ummarmu, kuma a yau suna son maimaita wannan tarihin da yaudara. Amma, tare da kasancewar al'umma mai ilimi da matasa masu hankali, abin ya ci tura. Mun kara karfi bayan kowace Matsala. A wannan karon, mutane za su taru don kare kimarsu.


 


Muna Gwagwarmaya Don Kare Lafiyar Mutane


 


Ya ci gaba da cewa: Wannan atisayen da aka fara a yau, domin nuna cewa muna fafutukar kare lafiyar jama’a ne, muna kuma aike da sako ga makwabtanmu cewa manufarmu ita ce abota da ‘yan uwantaka da kowa da kowa, amma wannan manufa za ta ci gaba muddin makiya ba sa so, sun kulla mana makirci kowace kasa da mulki suna hulda da mu daidai, mu ‘yan’uwa ne, muna son makwabtanmu su magance matsalolinsu tare ta hanyar farar hula da mu’amalar siyasa.


Idan Akai Barazana Ga Muradun Mu A Yankin, To Ba Mu Da Tsaka-tsaki


 


Babban kwamandan dakarun na IRGC ya jaddada cewa: Muna da muradu a wannan yanki, idan har sauyi ya faru a wani lungu da sako na yankin, kuma muradin mu suka shiga cikin hadari, to ba ma tsaka mai wuya, muna kare muradun kasa. Muna kare lafiyarmu kuma wannan ka'ida ce a gare mu kuma jan layinmu shine cewa babu abin da ya canza. Komai ya kamata ya dogara ne akan amincewa da ikon kasashe.


 


Muna ba da shawara ga kasashen da ke makwabtaka da su da kada su bari gwamnatin sahyoniya ta shiga cikin kasashen musulmi


 


Manjo Janar Salami ya ce: Muna son kowa ya warware matsalolin shi a hanyar tattaunawa. A duk inda gwamnatin sahyoniya ta ke, ita ce tushen rashin tsaro. Isra’ila ta kutsa kai cikin wasu kasashen kudu da yamma da arewacin kasarmu, suna iya cewa kasancewarsu ba shi da hadari ga tsaron kasarmu, amma manufar Isra’ila shi ne haifar da rashin tsaro.


 


Muna ba da shawara ga kasashen da ke makwabtaka da kasar da kada su bari Isra’ila ta shiga cikin kasashen musulmi, domin suna son warware rikicinsu a kasar Falasdinu da kuma neman haifar da rashin tsaro.


 


Ya kamata Al Saud ta daina buga wasannin kafafen yada labarai da matasanmu


 


A karshe babban kwamandan rundunar IRGC ya gargadi gwamnatin Saudiyyar inda ya ce: Ina bukatar mahukuntan Saudiyya da su yi taka tsantsan da halayyarsu, ku kuma sarrafa wadannan kafafen yada labarai da kamfanoni da kafafen yada labarai da ke yada farfaganda barna kawai da neman tada hankalin matasanmu, in ba haka ba kai kai zai koma kan mashekiya. Za mu karkare da kafa maku hujja. Kun shiga lamuranmu na cikin gida ta hanyar waɗannan kafofin watsa labarai, amma ku sani cewa kune zaku cutu. Don Haka Muna Cewa Da Ku Yi Hankali.