Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : iqna
Alhamis

22 Satumba 2022

21:04:45
1307389

Saudiyya za ta gina masallacin farko a kasar Cuba

Jakadan kasar Cuba a Saudiyya ya sanar da cewa, kasar za ta dauki nauyin gina masallacin farko ga tsirarun musulmin kasar Cuba.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na National cewa, jakadan kasar Cuba a kasar Saudiyya ya sanar da cewa, kasar za ta dauki nauyin gina masallacin farko a kasar Cuba domin yi wa musulmi tsiraru hidima.

Vladimir Gonzalez ya bayyana haka ne a wata hira da aka watsa a gidan talabijin na kasar Saudiyya inda ya ce: "Godiya da wannan tallafin kudi daga Saudiyya, a yau muna iya cewa muna gina masallacin farko a kasarmu a birnin Havana."

Ya kara da cewa: Muna da karamar al’ummar Musulmi a kasarmu. Suna da tsari sosai. Ina alfaharin sauƙaƙe rayuwarsu a matsayinsu na al'ummar Musulmi a Cuba.

Dangantakar diflomasiyya tsakanin Cuba da Saudiyya ta samo asali ne tun a shekarar 1956. Gonzalez ya ci gaba da cewa: Saudiyya ita ce kasar Larabawa ta farko da ta kulla huldar jakadanci da kasar Cuba.

Gonzalez ya kara da cewa asusun raya kasar Saudiyya ya ba da damar samar da ayyukan jin dadin jama'a da na tattalin arziki a kasar Cuba wadanda za su amfani kasashen biyu.

Ya zuwa yanzu dai kananan al’ummar musulmin kasar Cuba sun takaita ne da yin addu’o’i a gida ko kuma a wuraren sallar wucin gadi. A cewar rahoton cibiyar bincike ta Pew a shekara ta 2011, akwai musulmi 10,000 da ke zaune a Cuba, wanda ke da kasa da kashi 0.1% na yawan jama'a. Har zuwa shekarar 2012, galibin Musulman kasar Cuban ne da suka shiga wannan addini.


342/