Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

19 Satumba 2022

18:10:51
1306421

Shugaban Karbala: Ziyarar Arbaeen Ta Bana Ita Ce Mafi Girma A Tarihi

Gwamnan na Karbala ya bayyana cewa aikin ziyarar Arbaeen na bana shi ne mafi girma a tarihi, sannan ya kara da cewa: ‘yan sa kai 60,000 masu taimakawa ne suka halarci taron Arbaeen na bana tare da ba da hidima ga maziyartan.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Injiniya Nasif Jassim al-Khattabi, gwamnan Karbala ya sanar da cewa, Ziyarar Arbaeen ta bana (1444) ita ce Ziyarar Arbaeen mafi girma a tarihi.


A jiya Lahadi 27 ga watan Shahrivar shekara ta 1401 (21 Safar shekara ta 1444 H) a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin cikin gidan kasar Iraki Osman Al-Ghanimi ya jaddada cewa: Babu wani shirin tsaro da zai yi nasara ba tare da shirya matakan hidima, lafiya da sufuri ga masu ziyara ba.


Al-Khattabi ya bayyana cewa: Masu aikin sa kai 60,000 ne suka halarci aikin tattakin Arbaeen na bana, kuma sun halarci aikin ba da hidima ga masu ziyara.


Gwamnan na Karbala ya yi nuni da cewa, duk da goyon bayan da ma'aikatu da hukumomin kasar na sauran larduna suka bayar na samar da mafi kyawu ga miliyoyin masu Ziyarar, ma'aikatun hidima, tsaro da kiwon lafiya na lardin na fuskantar kalubale matuka wajen fuskantar wannan adadi mai yawan gaske.


Ya kamata a lura da cewa a wani kiyasi na farko, an ce Maziyarta miliyan 20 daga ciki da wajen kasar Iraki sun ziyarci Karbala a tattakin Arbaeen na bana, kuma adadin maziyarta ya karu da fiye da miliyan uku idan aka kwatanta da bara.


Wannan kuwa shi ne duk da cewa kasar Iraki - ciki har da garuruwanta da ake zuwa ziyararsu- ba su da kayayyakin more rayuwa; Amma duk haka mutuncin da karamar Ahlul Baiti (AS) da kokarin al'umma da jami'an wannan kasa ne kawai suka samar da sharuddan yanayi mai kyau na wannan adadi mai yawan gaske.