Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

16 Satumba 2022

18:47:30
1305970

Labaran Arbaeen Na Majalisar Ahalul Bayt As Ta Duniya

Rahoton Ayyukan Majalisar Ahlul Baiti (A) Ta Iraki A lokacin Arbaeen Shekara Ta 1444.

Daraktan Majalisar Ahlul Baiti (AS) na kasar Iraki ya bayyana cewa: A bana mun shirya jerin tawaga ta majalissar Ahlul-baiti (AS) a tanti na 833 "Akan Hanyar Ya Hussain (Najaf zuwa Karbala)". Baya ga tantanin majalissar, mun kuma gudanar da kafa wani tantanin na "Taron Ashurarl Na Kasa Da Kasa".

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa, a bana kamar kowace shekara, cibiyoyin addini, wa'azi, agaji, kiwon lafiya, hidima da tsaro a kasar Iraki suna kokari matuka wajen samar da ayyukan da suka wajaba ga miliyoyin al'umma Maziyarta Arbaeen Imam Husaini As.


"Majalisar Ahlul Baiti (A) Iraki" - na daya daga cikin majalisu na cikin gida da ke da alaka da majalissar Ahlul-Baiti (A) ta duniya - kuma daya ce daga cikin wadannan cibiyoyi da a kowace shekara suke gudanar da ayyuka da dama a sassa daban-daban na kasar domin hidima maziyartan gida da waje.


Daraktan wannan majalissar ya ce dangane da ayyukan na wannan shekara: Da albarkar Imam Zaman (A.S) mun samu rabauta a wannan shekara a zamanin Arba'in na 1444H domin yiwa Maziyarta hidima a fannin al'adu da wasu hidimomin.


Hujjatul-Islam al-Islam wal-Muslimin "Pahlwanzadeh Behbahani" wanda ya zanta da wakilin Abna ya kara da cewa: A bana mun shirya Tawaga ta mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) a tanti na 833 "Kan Hanyar Ya Hussain (Najaf zuwa Karbala).


Ya ci gaba da cewa: Baya ga tattakin majalissar, mun kuma gudanar da wani Tantin na “Taron Ashura na kasa da kasa”.


"Rarraba takardu ziyara da ke dauke da ziyarar Arbaeen da Ziyarar Ashura", "Rarraba Kasidu na Addini da Al'adu", " Gabatar da Littattafan Majalisar Ahlul Baiti (A.S),l ta duniya "Ayyukan Marigayi Ayatullahi Asefi", "Ayyukan Wa'azin". Malamai”, “Bayyana Falsafa, Buri da Sakamako na Motsin Imam Husaini (AS)” da “Amsa Shakku da Mas’alolin Shari’a” na daga cikin hidimomin al’adu da wadannan Tantina biyu ke yi wa maziyartan.


Malam Bahbahani ya kuma yi ishara da ayyukan jin dadin wadannan tantina guda biyu inda ya ce: A bana, saboda kasancewar miliyoyin Maziyarta daga kasashe daban-daban, an samu "gazawa" wanda hakan shi ne tsananin bukatar ruwan sha. A shekarun baya dai an fara gudanar da muzaharar Tattakin ne tsakanin ranakun 8 zuwa 10 ga watan Safar, amma saboda yawan maziyarta tun daga farkon watan Safar na bana. Don haka matsalar ruwan sha ta zama babbar matsala. Dangane da haka, tare da hadin gwiwar gidauniyar Ashura ta kasa da kasa, mun sayi ruwa mai dumbin yawa mai tsafta, kuma ya zuwa yanzu mun raba katan dubbai da dama ga maziyartan Masu yin Tattakin daban-daban.


Ya ci gaba da cewa: Ba da gudummawar magunguna da man shafawa ga masu Tattakin ke bukata zuwa "Asibitin Arbaini na Jami'ar Ahlul Baiti (AS) ta Karbala" wani hidima ne da muka yi tare da hadin gwiwar Mu'assasa Ashura.


Bahbahani ya ce dangane da mutanen da suke gudanar da tawagada tantunan guda biyu na Majalisar da Muassasar Ashura: Kimanin mambobi saba'in na "Heyat al-Zahra (S) Tehran" suna nan a karkashin kulawar Malam "Reza Almasi" kuma duk da mawuyacin halin da ake ciki. da karancin kayan aiki, suna hidima ga maziyartan Arbaeen


Har ila yau daraktan majalisar Ahlul-baiti (A) na kasar Iraki ya yi tsokaci kan hadin kai da taron kira na Aqsa inda ya ce: Tattakin Tawagoginmu guda biyu tana kusa da babban ginin jami'ar Ahlul Baiti (A) ta Karbala. Baya ga tarbar maziyartan Arbaeen da kafa asibitin, wannan jami'a tana gudanar da taron "Nida'ul Al-Aqsa" wanda a cikinsa akwai masu fafutuka da 'yan Sunna, wadanda suka fito daga Palastinu, Labanon da Siriya domin yi wa 'yan'uwansu Shi'a hidima a aikin Arba'in din Imam Husaini (a.s).


Hujjatul-Islam Islam Wal-Muslimin Bahbahani ya kara da cewa: An shirya cewa Halarta da bayanan Ayatullah Ramazani da babban sakataren kungiyar Ayatullah Akhtari shugaban majalisar koli da kuma Ayatullah "Dari Najafabadi" mataimakinsa. -Shugaban Majalisar Koli ta Majalisar Ahlul-Baiti (AS) ta duniya a Tarukan Nida'ul Al-Aqsa da sauran ayyukan Jami'ar Ahlul Baiti (A.S) zasu gudana a runfa ta 833.


Haka nan kuma ya ambaci hidimar da aka yi a tsakiyar ginin Majalisar Ahlul Baiti (AS) da ke birnin “Najaf Ashraf” inda ya ce: daruruwan maziyarta – daidaiku da iyalansu – sun ziyarci ginin Majalisar a Najaf kuma mun yi maraba da su. Sun yi kwana daya ko biyu a can sannan suka tafi Karbala ko kan iyakokinsu.