Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

25 Mayu 2022

18:07:13
1260899

​An Yi Tattaunawar Sirri Tsakanin Amurka Da Saudiyya Da Kuma Isra’ila

Kafofin yada labaran Amurka sun buga wani rahoto na wani babban dan jarida da ke zaune a Isra’ila game da yunkurin sasantawa da gwamnatin Biden ta yi tsakanin Saudiyya da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - A cewar rahoton da Barak Ravid ya fitar a shafin intanet na Axius, “idan sulhun da Amurka ke yi tsakanin Riyadh, Tel Aviv ya yi nasara,” za a dauki matakin farko na daidaita alaka tsakanin Saudiyya da Isra’ila.

Wasu majiyoyi biyar na Amurka da gwamnatinIsra’ila sun shaida wa kafafen yada labaran Amurka cewa, tattaunawar da Amurka ta yi ta shiga tsakani, ta hada da kammala mika mallakar wasu manyan tsibiran Masar guda biyu na Tiran da Sanafir da ke cikin tekun Red Sea ga Saudiyya.

A cewar Barak Ravid, idan aka cimma matsaya a sakamakon tattaunawar, hakan zai zama "wata muhimmiyar nasara ga manufofin ketare ga gwamnatin Biden a Gabas ta Tsakiya."

A cewarsu, fadar White House na son a cimma yarjejeniyar kafin ziyarar Joe Biden a yankin gabas ta tsakiya a karshen watan Yuni; Tafiyar da za ta hada hard a ziyarar Saudiyya da kuma Isra’ila.

342/