Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Laraba

29 Disamba 2021

20:01:14
1213545

Bidiyon Laftanar Janar Shahed Qasim Sulaimani Ya Na Ziyartar Kabarin Imam Ridha As

Bidiyon Ziyarar Haj Qasim Sulaimani Haramin Imam Ridha As.

Shahid Haj Laftanar Janar Qasim Sulaimani a lokacin rayuwarsa Yana cike da ayyuka na ruhiyya da Ma’anawiyya, Daga ciki har da ayyukan Ziyara a wurare masu tsarki na Ahlul Bait as.
An gudanar da wannan aiki ne a gefen aikinsa na kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) al-Quds.
A kwanakin baya ne shafin yanar gizo na Soleimani.ir ya saka wani hoton bidiyo na Laftanar Janar Qasim Sulaimani da ya ziyarci Haramin Imam Rida (a) a birnin Mashhad na lardin Khorasan Razawi.
Laftanar Janar Qasim Sulaimani da mataimakin kwamandan dakarun sa kai na Iraki Hashd al-Shaabi Abu Mahdi al-Muhandis sun yi shahada a wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai a filin jirgin saman Bagadaza da safiyar Juma'a 3 ga watan Janairun 2020.
Wasu sojojin IRGC (Pasdaran) hudu da ke rakiyar Laftanar Janar Sulaimani da wasu dakarun Hashd al-Shaabi hudu tare da Abu Mahdi al-Muhandis sun yi shahada a harin na sama da aka masu.
An binne gawar Shahid Sulaimani a makabartar Shuhada (Golzar-e Shohada) Kerman, Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Imam Ali bin Musa ar-Rida as, shi ne limami na takwas a cikin Imaman musulmi da Annabin Rahama SAWA ya barwa Al’ummarsa don suyi koyi dasu kuma tsatso na bakwai na Annabi Muhammad SAW. An haife shi a Madina a ranar 11 Zulqadah 138H.
Bayan rasuwar mahaifin Imam Rida, Imam Musa al-Kazim (as) ya ci gaba da aikin mahaifinsa a matsayin jagora ga Al’ummar musulmi.

Halifa Ma’amun na daular Abbasiyya wanda ke kan mulki a lokacin ya damu da tasirin Imam Rida a tsakanin musulmi. Don jawo hankalin jama'a da neman halasta ikonsa, sai halifa Ma’amun ya nada Imam Rida a matsayin Yarima mai jiran gado kujerar halifancin sa.
Haka nan an tilastawa Imam Rida (as) barin Madina da rayuwa a garin Maru dake arewa maso gabashin kasar Iran da nufin halifa Ma’amun ya mallaki tare sa ido ga dukkan ayyukansa da yake gudanarwa cikin sauki.
Sai dai burin Ma’amun na kawar da tasirin Imam Rida a kan musulmi bai cimma ba. Matsayin Imani da Ilimi da Dabi'u na Imam Rida (as) ya yi tasiri mai yawa a tsakanin al'ummar Khurasan har suka fahimci yanayin Ahlul Baiti Rasulullahi SAW.
Domin lalata martabar Imam Rida a cikin al'umma Ma’amun ya gayyaci malaman addini daban-daban domin su yi muhawara da mukabala shi. Duk da haka, bisa haƙiƙanin zurfin ilimin Imam Rida ya sa malaman addini sun yarda da gaskiyar wannan jikan Annabi Muhammad kuma sun sallama masa Daga karshe Ma’amun ya yanke shawarar kashe Imam Rida (as) ta hanyar sanya masa guba a shekara ta 203 Hijira.
Wani hadisi daga Imam Rida (a.s.) yana cewa “Wanda zai kusance ni a ranar kiyama shi ne wanda a duniya yake da kyakykyawan hali kuma ya fi kyautatawa iyalansa”.

342/