Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

22 Agusta 2021

12:44:42
1172086

Falasdinu: An Ji Karar Tashin Bama-Bamai A Zirin Gaza Bayan Wasu Hare-Haren Isra’ila

Rahotanni da suke fitowa daga yankin zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana cewa an ji karar tashin boma-bomai a yankin, bayan wasu hare-hare ta sama wadanda sojojin haramtaicciyar Isra’ila (HKI) suka kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Talabijin ta Presstv ta nakalto tashar talabijin ta Almayadeen ta lasar Lebanon na cewa, yahudawan sun kai hare-haren ne kan sansanin yan gudun hijira da Nuseirat da ke cikin lardin DeirAl-Balah na yankin.

Wadan nan hare-hare na zuwa ne, kwana guda kenan da wasu irinsu, wadanda sojojin yahudawan suka kai kan falasdinawa masu zanga-zanga a yankin.

342/