Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

28 Mayu 2021

14:18:58
1145147

Siriya : Bashar Al-Assad Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Shugaban Bashar al-Assad, na Siriya, ya lashe zaben shugabancin kasar a karo na 4.

Hakan dai zai bashi damar ci gaba da shugabancin kasar na tsawon wa’adin mulki na shekaru 7, masu zuwa.

Shugaban majalisar dokokin kasar Hamoudeh Sabbagh, ya ce Bashar al-Assad ya lashe zaben ne da kaso 95.1 na kuri’un da aka kada, sabanin kuri’u kaso 88.7 na shekarar 2014.

A ranar 17 ga watan Yulin 2000 ne shugaba Assad ya maye gurbin mahaifinsa Hafez al-Assad a matsayin shugaban kasa.

Karkashin kundin tsarin mulkin kasar na 2012, shugaban kasa na da damar tsayawa takara sau biyu, wanda ke nufin, wannan ne wa’adin shugaba Assad na karshe.

342/