Salami ya bayyana haka ne a wata harin da yayi da wata tashar talabijin a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, a bangaren tsaro boma-boma da facewa iri-iri na ta aukuawa a cikin kasar ba tare da gwamnatin ta bayyana dalilan aukuwarsu ba.
Daga cikin fashe-fashen dai akwai na tashar Jiragen sama na Bengerion, da ta kamfanin kirar makamai da kuma wadanda suke shafi jiragen ruwa a cikin ‘yan watannin da suka gabata. Har’ila yau ga fashewa ta Haifa da kuma kama jami’am Mosad a kasar Iraki da sauransu.
A bangaren siyasa kuma Janar Salami ya bayyana cewa bayan zabe har guda 4 ‘yan siyasar HKI sun kasa kafa gwamnatin wanda ya nuna babu wata nutsuwa a harkokin zamantakewa a kasar.
Ya ce a wasu wuare farin haramtacciyar kasar bai fi kilomita 14 kacal ba.
342/
