ABNA24 : Cibiyar ba da agaji ta Isra’ilan ce ta sanar da hakan a yau ɗin nan inda ta ce alal aƙalla mutane 44 sun mutu yayin da ake gudanar da taron Ibadan kana wasu kuma da dama sun sami raunuka wasu ma raunukan na su sun yi tsanani.
Turmutsutun dai ya faru ne lokacin da dubbun dubatan masu ibada suka taru a kasan tsaunin Meron da ke arewacin Isra’ilan don gudanar da bikin na ibada, inda wani waje da ɗimbin mutane ke tsaye a kai ya karye wanda hakan ya haifar da turmutsitsin a ƙoƙarin ficewa daga wajen da mutane suke yi.
Wasu rahotannin sun ce wannan shi ne wani taro mafi girma da aka gudanar a Isra'ilan tun ɓullar annobar korona.
342/
