-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Taron "Shahidul-Ummah" Imam Sayyid "Ali Khamene'i" (R.A) A Birnin Lahore Na Pakistan
Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: An gudanar da wani taro a ƙarƙashin taken "Shahidul-Ummah" a birnin Lahore na Pakistan, wanda ya tattauna gudummawa da gadon jagora shahidi Imam Sayyid "Ali Khamene'i" (R.A), tare da halartar dubban musamman daga kowane ɓangaren al'umma da sauran mazhabobin Musulunci a Pakistan.
-
Labarai Cikin Hotuna | Na Gudanar Da Tattaki Juyayin Shahadar Imam Hussain As A Garin Zaria Rana 1
A safiyar yau Talata 16/06/2026 Matasan Cikin Garin Zariya, Sun Futo Muzaharar juyayi, Wanda suke gabatarwa a duk Watan Ashura na ko wacce shekara, inda suke farawa tun daya daya ga wata har zuwa goma ga watan. kaman yanda kuke gani a Hotuna Matasan gasu sun sanya Bakaken riguna don Taya Manzon Rahma Jajen Abun da ya faru da Imam Hussain (AS) a filin Karbala.
-
Ma'aikatar Lafiya Ta Lebanon: Adadin Wadanda Sukai Shahada Sakamakon Hare-Haren Isra'ila Ya Kai 3,798
Adadin wadanda sukai shahada sakamakon ci gaba da hare-haren Isra'ila a Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris ya kai 3,798 da 11,781 da suka jikkata, bisa ga alkaluman da Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon da ta fitar a ranar Litinin.
-
Qalibaf: Ashura Makarantar Gwagwarmaya Ce A Gaban Zalunci
Shugaban Majalisar Shura ta Musulunci a wani sako da ya aika da shi a munasabar shigowar farkon watan Muharram, ya bayyana cewa wannan watan yana tunatar da jarumtaka, sadaukarwa da 'yanci, wanda al'ummar Iran, bisa rikonsu da daga koyarwar Ashura da tafarkin shahidai, za su tsaya tsayin daka a kan zalunci da wuce gona da iri, kuma za su ci gaba da tafarkin daraja da tsayin daka.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Dora Tutar Juyayin Imam Husaini As A Haramin Sayyidah Fatima Ma’asumah (S)
Yayin da watan Muharram ke gabatowa, a yammacin jiya Litinin (15 ga Yuni, 2026), a wani taroi da ya tara dimbin masu ziyara da mazauna yankin, a farfajiyar Imam Raza (As), da ke haraim Sayyidah Fatimah Ma’asumah As an daga tutar baƙin ciki da juyayin Imam Husaini As a kan kubbar harami mai tsarki na Haramin Sayyidah Fatima Ma’asumah (S).
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Dora Tuta Mafi Girman A Makokin Imam Husaini As A Tehran
An gudanar da taron daga mafi girman tutar makokin Imam Husaini As a ƙasar Iran a saman hasumiyar Jamhuriyar Musulunci, a yankin al'adu da yawon bude ido na Abbas Abad a Tehran.
-
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H): A Muhimmantar Da Sanya Baƙaƙen Tufafi A Zaman Ashura
Muna so ne mutun ya rinƙa yin abin da ya dace da kansa‚ ba sai an zungureka ba. Kamar yadda Amirul Muminin (a.s) yake cewa: Dabba ita ce sai an zungureta‚ mai hankali kuwa hankali ya isa ya nuna masa abin da ya dace. Gani ga wane ya isa ishara ga mai hankali. Wannan faɗin Amirul Muminin (a.s) ne.
-
Shekh Zakzaky: Al-Muharram Watan Da Aka Keta Hurumin Manzon Allah Da Iyalansa Tsarkaka Ta Hanyar Shekar Da Jinainensu
An kira shi Al-muharram ne saboda Allah ta'ala ya haramta shi. Wato haramun ne a yi yaƙi a cikinsa, yana da alfarma a wajen Allah. To, kuma har a jahiliyyah sun kasamce suna kulawa da alfarmar watanni masu alfarma.