-
Labarai Cikin Bidiyo | Muzaharar Don Nuna Goyon Baya Ga Alƙur'ani Da Masallacin Al-Aqsa A Sana'a
Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait (AS) - ABNA - ya ruwaito cewa: miliyoyin mutanen Yemen sun fito kan titunan Sana'a, babban birnin Yemen, a wata zanga-zanga mai girma, inda suka nuna goyon bayansu ga al'ummar Falasdinu da Lebanon, suka kuma yi Allah wadai da cin mutuncin da ake yi wa Alƙur'ani Mai Girma da wuraren tsarki na Musulunci. Wasu daga cikin mahalarta taron, suna ɗauke da Alƙur'ani da makamai, suna ta shelanta taken adawa da Amurka da kuma gwamnatin Isra'ila
-
Isra'ila Ta Kai Harin Bama-Bamai Mai Tsanani A Jabaliya
Dakarun Isra'ila sun kai hare-hare biyu ta sama a yammacin ranar Litinin a yankin Falouja a sansanin 'yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza, lamarin da ya haifar da barna mai yawa a gidaje da kewayen yankin, wanda a baya ya sha barna mai girma sakamakon ci gaba da yakin da ake yi a yankin.
-
Mujallar Foreign Affairs: Sansanonin Amurka Sun Zama Nauyi A Kan Yankin Farisa
Mujallar Foreign Affairs ta Amurka, a wani dogon bincike na mai bincike David B. Roberts, mataimakin farfesa a fannin nazarin Gabas ta Tsakiya a Kwalejin King's ta Jami'ar Landan, ta tabbatar da cewa yakin Amurka da Isra'ila akan Iran ya sanya kasashen tekun Farisa a cikin wani sabon yanayin tsaro wanda ta bayyana a matsayin "wanda ba za a iya jurewa ba," tana nuna cewa kasancewar sojojin Amurka da kasashen yankin Tekun Farisa suka dogara da shi shekaru da yawa ya rikide daga wani batun kariya zuwa tushen barazana kai tsaye, bayan da sansanonin Amurka da aka baza a yankin suka zama babban dalilin hadafi ga ababen more rayuwa na kasashen da cibiyoyin mai da otal-otal ga hare-haren Iran da ka iya faruwa.
-
Jami'ai: 'Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai 39 Kuma Suka Kashe Malami A Jihar Oyo A Najeriya
Hukumomin Najeriya sun bayyana a jiya Litinin cewa 'yan bindiga sun sace akalla ɗalibai 39 da malamai bakwai a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, suka kashe daya daga cikin malaman, tare da raunata jami'an tsaro ta hanyar amfani da bama-bamai a lokacin ƙoƙarin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
-
Mutane 4 Sun Mutu A Zanga-Zangar Adawa Da Hauhawar Farashin Man Fetur A Kenya
Ministan cikin gida na Kenya, Kipchumba Murkomen, ya bayyana cewa mutane huɗu sun rasa rayukansu a jiya Litinin a zanga-zangar da aka yi a garuruwa da dama na Kenya don adawa da hauhawar farashin man fetur sakamakon yaƙi da Iran, bayan da yajin aikin gama-gari a fannin sufuri na jama'a ya bar matafiya a makale.
-
Ɗaliban Fudiyya Sun Yi Mauludin Imam Ali Ridha (as) A Garin Yelwa Mai Bene + Hotuna
A jiya Litinin 18/05/2026, ɗalibai Yara Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), na makarantar Fudiyya da ke garin Yalwa Mai Bene, ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna, sun gudanar da Mauludin Imam Ali Arridha (as)
-
Iran Ta Lalata Rukunin Sojojin Amurka 228 A Fadin Sansanonin Tekun Farisa
Hotunan tauraron dan adam, tare da rahoton da aka danganta ga jaridar Washington Post, an buga su suna nuna cewa Iran ta kai wani mummunan hari kan rukunin sojoji 228 na Amurka a yankin Tekun Farisa.
-
Mafarkin Kaiwar Farshin Mai Dala 180 Zai Tabbata Tare Da Koma Bayan Tattalin Arzikin Duniya
Ƙasashen Duniya 80 Sun Shiga Shirin Ko Ta Kwana Sakamakon Tabarbarewar Makamashi A Yaƙin Da Iran
Masana sun yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da dakatarwa da hana fitar da mai ta mashigar Hurmuz, farashin mai zai sake yin tsallen badahu mai girma da ba a taɓa ganin irinsa ba.
-
Kudaden Da Amurka Ta Kashe A Yakin Ta Iran Ya Haura Dala Biliyan 85 A Cikin Kwanaki 79
Kudaden da Amurka ta kashe a yakin da take yi kan Iran sun haura dala biliyan 85 a cikin kwanaki 79 da fara yakin, kamar yadda bayanai daga shafin Iran War Cost Tracker suka nuna, wanda ke lura da bibiyar qididdigar asarar kudaden da ake kashewa a yakin.
-
Yaƙin Iran Jawo Asarar Biliyoyin Daloli Ga Tattalin Arzikin Duniya Ga Sassan Jiragen Sama Da Motoci
Rahotanni na tattalin arziki sun bayyana cewa yaƙin da Amurka da Isra'ila suke yi wa Iran ya jawo asara da ƙarin kuɗaɗe masu yawa ga kamfanonin duniya, wanda ya haura dala biliyan 25 har ya zuwa yanzu, yayin da fargaba ke ƙaruwa game da tasirin tattalin arziki mai faɗi a kasuwannin duniya da sassan makamashi, sufuri da masana'antu.
-
Rahoto Cikin Hotuna | Na Taron Tunawa Da Shahid Dokta Ali Larijani A Masallacin "Bilal" Tehran
Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: An gudanar da taron tunawa da Shahidi Dokta Ali Larijani a yau 18 ga Mayu 2026 a masallacin Bilal na gidan talabijin da rediyo na Iran, tare da halartar manyan hafsoshi na soji da na kasa, da kuma gungun manajoji da ma'aikatan kafofin yada labarai na kasa.