Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar gidan yanar gizon, wannan adadi ya hada da kudaden da ake kashewa wajen samar da abinci da kayan more rayuwa ga sojoji da jiragen ruwa da aka tura yankin, da sauran kudaden da ke da alaka da hakan.
Wannan kididdigar ta ninka sau uku a kan adadin dala biliyan 29 wanda kwanakin baya Jules Hurst, mukaddashin darektan kudi na Pentagon, ya bayyana.
Wannan shafin yanar gizon wanda masu bincike a dakin gwaje-gwaje na magance matsalolin yanayi a Jami'ar Brown ta Amurka ke gudanarwa, wanda ke lura da girma da asarar da yakin ke haifarwa ga masu amfani da kayayyaki a Amurka sakamakon hauhawar farashin makamashi, ya bayyana cewa hauhawar farashin man fetur da kashi 51.4% da kuma na dizal da kashi 53.4% ya jawo wa 'yan kasa asarar sama da dala biliyan 42 har ya zuwa yanzu, wanda ke nufin kusan dala 322.47 ga kowane iyali a Amurka.
Your Comment