(ABNA24.com) ‘Yan sandan kasar Amurka a jahar Montana sun sanar da cewa mutane uku ne aka kashe yayin da wani guda daya ya jikkata.
Tashar talabijin din IBC News ta ambata cewa; Wani dan bindiga ne ya bude wuta akan mutanen da su ke cikin wani gidan rawa a garin Great Falls da ke jahar Montana,inda nan take mutane uku su ka mutu, yayin da wani daya ya sami raunuka.
Harbi akan mai uwa da wani a kasar Amurka ya zama ruwan dare, inda daga lokaci zuwa lokaci ‘yan bindiga dadi su ke yi wa mutane kisan kiyashi.
Gwamnatoci daban-daban na kasar Amurka sun kasa daukar matakai akan hana ko kayyade halarcin sayar da makamai ga mutane, saboda karfin tasirin da kungiyar masu dauke da makamai take da shi a fagen siyasar kasar.
/129
Mutane 4 Ne Su Ka Mutu Da Kuma Jikkata Sanadiyyar Bude Wutar Da Aka Yi A Jahar Montana Ta Kasar Amurka
18 Disamba 2019 - 06:01
Lambar labari: 994741
‘Yan sandan kasar Amurka a jahar Montana sun sanar da cewa mutane uku ne aka kashe yayin da wani guda daya ya jikkata.