14 Disamba 2019 - 04:38
Makiya Na Da Hannu Wajen Yada karya A Zanga- zangar Adawa Da Karin Farashin mai A Iran

Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasa Ali Shamkhani shi ne ya bayyana haka a sa’ilin da ya ziyarci iyalan wadanda tarzomar da aka yi a lokacin kara farashin man fetur a baya bayan nan a kasar, ...

(ABNA24.com) Babban sakataren Majalisar koli ta tsaron kasa Ali Shamkhani shi ne ya bayyana haka a sa’ilin da ya ziyarci iyalan wadanda tarzomar da aka yi a lokacin kara farashin man fetur a baya bayan nan a kasar, inda ya bayyana cewa sama da kaso 85% na wadanda abin ya rutsa da su a lokacin tarzomar a binin Tehran ba sa cikin zanga -zangar da aka gudanar, kuma an kashe wasu ne cikin wani yanayi da ke cike da shakku da makami kanana da manya.

Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani da gwamnati ta fitar na adadin wadanda lamarin ya shafa tsakanin mutanen gari da kuma jami’an tsaro, kana ya fadi cewa gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a kasar suna bakin kokarinsu wajen ganin sun tattafawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Idan ana iya tunawa jim kadan bayan afkuwar tarzomar jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamina’i ya umarci majalisar koli ta tsaron kasa da ta shirya rahoto game da musabbabin abin da ya haifar da tarzomar da kuma bada taimakon gaggawa ga iyalan wadanda abin ya shafa.

A bangare guda kuma jakadan Iran a kasar Birtaniya ya zargi gidan talbijin din BBC mai watsa shirye shriyensa da harshen Parisanci da hannu goyon bayan Amurka kan takunkumin taadancin tattalin arziki da ta kakabawa kasar Iran ta hanyar nuna munanan hotunan karya game da halin da kasar ke ciki da kuma tunzura alummar kasar don kwashe dukiyarsu dake bankunan kasar.




/129