(ABNA24.com) Babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo janar Bagheri ya bayyana cewa Iran na taimakawa dakarun tsaron kasar Yemen da masu bayar da shawara, kuma ina tunanin cewa wannan nauyi ya rataya ne a kan Dakarun juyin juya halin musulinci, sannan za su ci gaba da taimakawa al’ummar kasar Yemen har zuwa lokacin da aka kawo karshe hare-haren wuce gona da ake kai musu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto babban hafsan hafsoshin sojin Iran Manjo janar Muhamad Bagheri yayin da yake amsa tamboyoyin manema labarai kan harakokin tsaro na cewa haki ne kan dakarun juyin juya halin musulinci su taimakawa duk wata al’ummar musulmi da ake zalinta, don haka muka ga ya dace mu taimakawa al’ummar kasar kasar Yemen da Sojoji masu bayar da shawara.
Yayin da ya koma kan kasar China, Bagheri ya ce yayin ziyarar da ya kai kasar China, an gabatar da shawarwarin kan fadada alaka tsakanin kasar ta China da jamhoriyar musulinci ta Iran
Kuma kasar Iran ta amince da fadada alakar tsaro tsakanin da kasar ta China, don bayan mun dawo birnin Tehran, mun sanya hanu kan wasu yarjejeniya tare da mika su zuwa ma’aikatar harakokin waje, inda su kuma za su mika su zuwa ga ofishin jakadancin kasar China dake nan.
/129
2 Oktoba 2019 - 04:59
Lambar labari: 979763
Babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran Manjo janar Bagheri ya bayyana cewa Iran na taimakawa dakarun tsaron kasar Yemen da masu bayar da shawara, kuma ina tunanin cewa wannan nauyi ya rataya ne a kan Dakarun juyin juya halin musulinci,...