29 Satumba 2019 - 04:38
Ruhani:Kasashen Turai Sun Tabbatar Da Cewa Basu San Wanda Ya Kai Hare-Hare Kan Aramco Ba

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa kasashen Turai basu san wadanda ya kai hare-haren kan kamfanin Aramco na kasar Saudiya ba.

(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa kasashen Turai basu san wadanda ya kai hare-haren kan kamfanin Aramco na kasar Saudiya ba.

Tashar talabin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a bayan dawowarsa daga taron babban zauren majalisar dinkin duniya a birnin New York na kasar Amurka.

Rahuni ya kara da cewa ya tambayi shuwagabannin kasashen turai day a hadu da su a New York kan cewa da wani dalili ne suke tuhumar Iran da kai hare-hare kan Amurka, wasunsu suka ce, bisa bayanai na kwararrau, da kuma cewa kungiyar Huthi bas u da karfin kai irin wadannan hare-hare masu karfi.

Shugaban sai ya ce, sai na tambayesu way a kai harin, sai suka ce basu sani ba.

Shugaban ya kara da cewa da farko shuwagabannin kasashen na Turai don sune suke sayarwa kasashen larabawa makamai, sannan basu san su waye yan kasar Yemen bas hi yasa suke tuhumar Iran da kai hare-haren.


/129