(ABNA24.com) Shugaban na kasar Amurka Donald Trump wanda yake mayar da martani akan matakin da kasar Faransa ta dauka na kara kudin haraji akan kamfanoni fasaha da kimiyya na kasashen waje da suke aiki a cikin kasar, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Wautar da Macron ya yi za ta jawo mayar da martani akan kasarsa.
Shugaban na kasar Amurka ya kuma yi gargadin cewa; Abu ne mai yiyuwa a kara yawan kudaden fito akan hajar da kasar ta Faransa take kerawa.
Majalisar dokokin kasar Faransa ta amince da kara kudaden harajin akan manyan kamfanonin fasaha na waje da suke a cikin kasar da su ka hada da Google, Facebook da Amazon.
Gabanin wannan lokacin, kamfanoni irin wadannan ba su biyar kudaden haraji a cikin kasa kamar Faransa. Kamfanonin da biyan harajin zai shafa, su ne wadanda su ke da kudin shiga a duniya baki daya da su ka haura Euro miliyan 750, kuma a cikin faransa suke samun fiye da euro miliyan 25.
/129
29 Yuli 2019 - 03:50
Lambar labari: 965478
Shugaban na kasar Amurka Donald Trump wanda yake mayar da martani akan matakin da kasar Faransa ta dauka na kara kudin haraji akan kamfanoni fasaha da kimiyya na kasashen waje da suke aiki a cikin kasar, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa; Wautar da Macron ya yi za ta jawo mayar da martani akan kasarsa.