(ABNA24.com) Takunkuman zasu shafi wasu daidaikum mutane ne da aka tantance, da Amurkar, ta ce su ne ummul’aba’isin rikice-rikicen da aka samu yayin zabukan kasar.
Amurkar dai bata fayyace karara sunaye mutanen da takunkumin ya shafa ba, ko kuma sharudan da zata amfani dasu ba wajen hana masu Vizar ba.
Amma sanarwar ta ce takunkumin zai shafi wasu mutane ne, ba wai al’umma na ko kuma gwamnatin Najeriya.
Wannan ba shi ne karo na farko ba da Amurka ke kakaba irin wannan takunkumi ba, inda ko a shekara 2015, data gabata, yayin wata ziyara da ya kai Najeriya, sakataren harkokin waken Amurkar, na waccen lokacin John Kerry, ya yi alkawarin hana viza ga duk wani mutum da aka samu a hannu a rikicin siyasar Najeriyar, saidai tun lokacin gwamnatin Amurkar bata aiwatar da wannan matakin ba.
Saidai tuni wasu suka fara danganta lamarin da cewa zai oya kasance yadda ake ci gaba da samun tabarbarewar dangantaka tsakanin gwamnatin Shugaba Buhari da kuma tawagar jami’an diflomatsiyya na Amurka a Najeriya.
/129