A game da zaben ‘yan majalisar dokoki kuma, daga cikin ‘yan takara 15. 505 da suka gabatar da takardunsu 282 kawai ne, hukumar zaben Ceni ta amince da takararsu
Eve Bazaiba, babban sakataren MLC, jam’iyar Jean-Pierre Bemba, da ajiya ya gudanar da wani taro da daukacin yan takarar dake son tsayawa a karashin jam’iyarsa, inda ya sanar da RFI matukar bacin ransa kan matakin da hukumar zaben ta dauka.
Inda ya ce a ganin sa, takarar Jean-Pierre Bemba ce ta firgita bangare shugaba Kabila har, suka karkatar da hukumar zaben ta dau matakin korarsa a takarar ta Mr Bemba
Tuni dai yan adawa suka yi kiran gudanar da zanga zangar nuna rashin amincewa da mataki
Ana dai ganin Mr Jean-Pierre Bemba da ba a jima ba kotun duniya ta wanke shi, bayan share tsawon shekaru 11 a tsare kan zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama da sojojinsa suka yi a kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a matsayin daya daga cikin yan takarar da za su iya lashe zaben.
25 Agusta 2018 - 16:12
News ID: 906827

A jamhuriyar demokradiyar Congo hukumar zaben kasar ta kori yan takara 6 daga cikin 25 dake bukatar tsaya wa a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar 23 ga watan desembar wannan shekara 2018 ‘Yan takarar da aka kora, sun hada da daya daga cikin manyan yan adawar shugaba Josèphe Kabila, cewa da Jean-Pierre Bemba, a kan laifin gabatar da shaidun karya a shara’arsa ta kotun duniya, da kuma tsohon fara ministan kasar Antoine Gizenga, da Adolphe Muzito da Sami Badibanga, sai Jean-Paul Moka-Ngolo da kuma uwargida Marie Josée Ifoku.