A kowace shekara dai 'yan Shi'a suna gudanar da bukukuwan juyayin Tasu'a din da ta fado a ranar 9 ga watan Muharram, don tunawa da irin zaluncin da Banu Umayya suka yi wa Imam Husain (a.s) jikan Annabi kuma Imamin Shi'a na uku'yan Shi'a, da mabiyansa a Karbala a shekara ta 680 miladiyya.
Miliyoyin 'yan Shi'a din ne dai cikin bakaken kaya da sauran nau'oi na nuna bakin ciki da juyayi suke fitowa kan tituna da kuma taruwa a wajajen ibada don nuna juyayinsu inda kuma malamai da mawaka suke bayanin abubuwan da suka taru ga Imam Husain (a.s) da sauran zuriyar Annabi din.
A gobe Lahadi ne dai ake sa ran za a gudanar da bukukuwan juyayin Ashura, wato ranar da Imam Husaini (a.s) da mabiyansa su 72 suka yi shahada cikin mafi munin yanayi a Karbala a shekara ta 61 bayan hijirar Ma'aiki (a.s)