25 Afirilu 2017 - 10:47
Jagora Yayi Afuwa Wa Fursunoni 593 Don Murnar Zagayowar Ranar Aiko Manzo (s)

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi afuwa ga wasu fursunoni da kuma rage wa wasu hukuncin da aka yanke musu na zaman gidan yari don murnar zagayowar ranar da aka aiko Ma'aikin Allah (s) a matsayin Annabi kuma Manzo ga dukkanin talikai.

A wata sanarwa da ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fitar a jiya din nan Litinin an bayyana cewar Ayatullah Khamenei ya amince da bukatar da shugaban Ma'aikatar shari'a kuma alkalin alkalai na Iran Ayatullah Sadeq Amoli Larijani ya gabatar masa na yin afuwa ko kuma rage hukuncin zaman gidan yari da aka yanke wa wasu fursunoni 593.

A cikin wasikar wa Jagora Imam Khamenei, Ayatullah Larijanin ya bukace shi da yayi afuwa ga wadannan fursunoni don murnar zagayowar ranar Mab'ath, wato ranar da aka aiko Annabi (s) a matsayin manzo.

Ranar 27 ga watan Rajab, hijiriyya dai ita ce ranar da aka aiko Ma'aikin Allah (s) a matsayin Annabi kuma Manzo ga dukkanin talikai, a saboda haka ne a Iran da ma wasu kasashen musulmi ake gudanar da bukukuwan murnar wannan rana mai tarin albarka.