Majalisar ta ce, sojojin sun yi amfani da manyan bindigogi masu sarrafa kansu wajen kashe ‘ya tawayen.
Mai magana da yawun Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Liz Throssell ta ce, sojojin sun yi amfani da manyan bindigogi masu sarrafa kansu wajen tarwatsa ‘yan tawayen da ke dauke da addina da karafa.
Throssell ta ce, sun damu matuka game da alkaluman mamatan, wadanda in aka tabbatar da gaskiyarsu, hakan na nuni da yadda sojojin suka yi amfani da karfin da ya wuce kima kan ‘yan tawayen.
A ‘yan watannin nan dai, daruruwan mutane sun rasa rayukansu yayin da dubbai suka rasa muhallansu a tsakiyar kasar ta Jamhuriyar Democradiyar Congo sakamakon arangama tsakanin jami’an tsaro da kuma ‘yan tawayen da ke neman daukan fansar kisan shugabansu Kamwina Npasu.
A cikin watan Agustan bara ne sojojin Congo suka kashe jagoran ‘yan tawayen bayan ya lashi takobin shafe jami’an tsaro da ke lardin Kasai, bayan ya zarge su da cin zarafin al’umma.
Mai magana da yawun hukumar kare hakkin dan adam ta MDD Liz Throssell ta ce, tun bayan kashe Npasu ne ‘yan tawayen suka kudiri tsaurarran akidu, abin da ya sa suke kai faramaki kan kadarorin gwamnati.,
A bangare guda kuma, wasu masharhanta sun ce, rikicin Congo ya tsananta ne tun bayan da shugaba Joesph Kabila ya ki sauka daga kujerarsa duk cewa wa’adainsa ya kawo karshe a cikin watan Disamban da ya gabata.288