5 Nuwamba 2016 - 15:00
Mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Najeria 5

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta biyar, da suka hada da wani mai mukamin Laftanar Kanar, lokacin da suka dakile wani harin mayakan Boko Haram a kan barikin sojin kasar na 119 dake Mallam Fatori, jihar Borno.

Cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin kasa ta kasar, Kanar Sani Uman Kukasheka, ya ce sojojin sun kashe mayakan Boko Haram din goma sha hudu a lokacin artabun.

Ya ce wasu sojojin hudu kuma sun samu raunuka a harin wanda mayakan kungiyar suka kai a daren Juma'a.

Kanar Kukasheka ya ce cikin makaman da sojojin suka kwace daga wurin mayakan sun hada da babbar bindiga samfurin GPMG, da AK-47 guda bakwai da kuma albarusai da dama.

Kakakin sojin ya kuma ce ana ci gaba da aikin kakkabe mayakan Boko Haram din daga yankin.

A 'yan kwanakin nan dai, 'yan bindiga da ake gani mayakan Boko Haram ne sun yi ta yunkurin kai hare-hare a sassan jihar Borno da dama.

Ko a karshen watan Oktoba, sojojin Najeriyar biyar da 'yan sintiri uku da dan kato da gora daya sun rasa rayukansu lokacin da mayakan Boko Haram din suka yi musu kwanton bauna a kauyen Ugundiri dake karamar hukumar Damboa.

Sojoji sha tara kuma da dan kato da gora daya sun sami raunuka a kwanton baunar.288